Kasashe 25 na duniya masu karfin iko a 2019
Abin mamakin shine kasar Amurka ce ta kasance kasa mafi karfin iko a duniya a wannan shekarar, kamar yadda labaran Amurka da kuma rahoton duniya na 2019 ya nuna. Tana biye ne da kasar Rasha, China da Jamus.
Amurka ta fito a na daya ne jerin nan saboda tana da kasafi mafi girma na soji da kuma tattalin arziki a duniya. A don haka ne aka kwatanta ta da "mafi rinjaye a tattalin arziki kuma mafi karfin iko a duniya."
Manyan kasashen a duniya mafiya rinjaye kamar yadda rahoton ya nuna su ne: Amurka, Rasha, China, Jamus, UK, Faransa, Japan, Isra'ila, Saudi Arabia da kasar Korea ta Kudu.
Wannan binciken ya ta'allaka ne a kan mulki, rinjayen tattalin arziki, rinjayen siyasa, dangantaka da kasashen duniya da karfin rundunar soji.
DUBA WANNAN: Tirkashi: An kama Dino Melaye yana siyan kuri'u (Hoto)
Kasashen da aka ba wa wannan matsayin sun kai kasashe 80, inda a ka zakulosu daga kasashe 193 da suke mambobin majalisar dinkin duniya.
Ga jerin kasashe 25 na duniya mafiya rinjaye a duniya a 2019.
1. Amurka
2. Rasha
3. China
4. Jamus
5. Ingila
6. Faransa
7. Japan
8. Isra'ila
9. Saudiyya
10. Korea ta Kudu
11. Hadaddiya Daular Larabawa (UAE)
12. Canada
13. Iran
14. Switzerland
15. Australia
16. Turkey
17. India
18. Italy
19. Iraq
20. Singapore
21. Sweden
22 .Pakistan
23. Spain
24. Qatar
25. Belgium
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng