Kwallon kafa: Wenger ya zama Shugaban wata hukuma a karkashin FIFA

Kwallon kafa: Wenger ya zama Shugaban wata hukuma a karkashin FIFA

Tsohon Mai horas da ‘yan wasan kungiyar Arseanal ta Ingila, Arsene Wenger, ya koma aikin wasan kwallon kafa bayan ya amince da wani tayi da hukumar FIFA ta Duniya ta yi masa.

Kamar yadda mu ka samu labari da yammacin Ranar Larabar nan, tsohon Kocin mai shekaru 70 da haihuwa ya zama shugaban hukumar cigaban wasan kwallon kafa na Duniya baki daya.

Kungiyar kwallon kafa ta FIFA ce ta zabi Kocin da ya bar aiki a tsakiyar shekarar 2018 domin ya ja ragamar wannan hukuma. FIFA ta yi wannan jawabi ne a shafinta a Ranar 13 na Nuwamba.

Arsene Wenger wanda ya shafe shekaru 22 a Arsenal, ya tabbatar da cewa ya karbi wannan aiki inda ya fito ya na mai cewa: “A shirya na ke domin shiga kalubalen wannan muhimmin aiki.

KU KARANTA: Van Dijk, Messi, Salah, Ronaldo, Mane su ne Taurarin bana

Wannan ya kawo rade-radin da ake yi na cewa zai koma horaswa a kungiyar Barcelona ta Sifen ko kuma Bayern Munich da ke Garin Munchen. Wenger ya lashe kofi kusan 10 da ye ke Arsenal.

A wannan sabon aiki da Arsene Wenger zai fara, nauyin kawo cigaba a harkar kwallon kafa na maza da mata a Duniya ya rataya ne a kansa kamar yadda jawabin da aka fitar dazu ya nuna.

Haka zalika Wenger ya na da alhakin kawo sababbin fasaha a Duniyar kwallo. Wannan kujera da ya hau ta na nufin ya shiga cikin sahun kwamitin fasaha na majalisar kwallon kafa na Duniya.

Bugu da kari daga yanzu Mista Arsene Wenger wanda ake yi wa lakabi da La-Professor watau Shehin kwallon kafa ya zama shugaban kwamitin FIFA da ke lura da fasahar wasan kwallo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng