Jamila Nagudu ce tafi cancanta a bawa gwarzuwar shekara ba Fati Washa ba - In ji Kamaye na Dadin Kowa

Jamila Nagudu ce tafi cancanta a bawa gwarzuwar shekara ba Fati Washa ba - In ji Kamaye na Dadin Kowa

Fitaccen marubuci kuma jarumin fina-finan Hausa Dan'azumi Baba Cediyar 'Yan Gurasa wanda aka fi sani da kamaye ya bayyana cewa jaruma Jamila Nagudu ce tafi cancanta ta zama gwarzuwar shekara a masana'antar Kannywood ba Fati Washa ba

A wani labari da muka samu a tashar Tsakar Gida ta shafin YouTube ta bayyana cewa fitaccen marubuci kuma jarumin fina-finan Hausa Dan'azumi Baba Cediyar 'Yan Gurasa wanda aka fi sani da kamaye ya bayyana cewa jaruma Jamila Nagudu ce tafi cancanta ta zama gwarzuwar shekara a masana'antar Kannywood ba Fati Washa ba.

Kamaye ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa a matsayinsa na marubuci, mai shirya fina-finai kuma jarumi, tabbas Jamila Nagudu ce ta cancanci zama gwarzuwar Kannywood.

KU KARANTA: Hukunci ko azaba: Wani ya kulle kanwarsa a daki na tsawon shekara biyu a jihar Kaduna

Inda yayi rubutu kamar haka: "To gaskiya ba zan iya cewa komai a game da rashin samun gwarzuwar Jaruma ga Jamila Nagudu ba, amma dai tabbas! Na san Jamila Nagudu ta iya duk abin da ake so a harkar fim. In dai Hausa fim ne ta kere sa'a. To amma watakila a gurin masu zaben ne su ke ganin bata cancanta ba. Amma ni dai a matsayina na marubuci, mai shirya fina-finai, mai bada umarni kuma jarumi, wallahi tuni Jamila Nagudu ta gama cancanta da ta samu gwarzuwar jaruma. Domin babu gurin da za a sakata a cikin fim din Hausa ba ta yi abin da ya cancanta ba.

"Don haka babu karya, Jamila Nagudu wallahi ta iya, kuma ta cancanta da duk wata karramawa da za a baiwa kowacce irin jaruma."

Wannan batu na jarumin dai ya biyo bayan fitacciyar jarumar nan Fatima Abdullahi wacce aka fi sani da Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jaruman fina-finan Hausa a wani bikin fina-finan Afirka da aka yi a kasar Birtaniya makon da ya gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel