Aisha Buhari ta shirya taron addu’o’i a fadar Shugaban kasa, ta yi kira ga Iyaye

Aisha Buhari ta shirya taron addu’o’i a fadar Shugaban kasa, ta yi kira ga Iyaye

Uwargidar Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta shirya taron addu’o’i da aka yi wa Najeriya. An zuba addu’o’in ne domin magance matsalolin da ke kawowa cigaban kasar cikas.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, an gudanar da wannan zaman addu’o’i ne a Ranar Litinin, 11 ga Watan Nuwamba, 2019. Wannan ya zo daidai lokacin da Musulman Duniya ke bikin Mauludi.

Matar Shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta yi jawabin gabatarwa a wajen zaman da aka yi inda ta ce addu’o’i ne jiragen da Bayi ke hawa domin mikawa Ubangiji bukatu, kuma Ya amsa.

“Musulunci ya zayyano nauyin da ke kanmu wajen Mahallicinmu, da al’ummarmu, da ‘Yanuwanmu na kusa da nesa, kuma dole mu sauke wannan nauyi bakin gwargwadon karfinmu.”

Uwargidar shugabar Najeriyar ta kuma yi kira ga Mazaje wanda su ne shugabanni da su rike koyarwar Manzon Allah watau Annabi Muhammad SAW ta hanyar sauke dawainiyar iyalinsu.

A cewar Matar shugaba Buhari, addu’o’in da aka yi za su taimaki Najeriya na tsawon shekaru tare da taimakawa wajen kawo karshen matsalolin da su ka dabaibaye Najeriya, su ka hana ta cigaba.

KU KARANTA: Shekau ya aikowa Masu Mauludin Manzon Allah wani sako

A shafin na ta Tuwita, Aisha Buhari, ta tabbatar da wannan zama da aka yi da Malaman addinin Musulunci Ranar Litinin, inda ta ce: “Yau na shirya taron addu’o’i na musamman ga Kasar nan.”

Mai girma Hajiya Buhari ta kara da cewa: “Mun duba tasirin addu’o’i wajen cigaban al’umma. Taron ya samu halarcin manyan malaman addinin musulunci daga wurare dabam na fadin kasar”

A jawabin Matar shugaban na Najeriya ta kuma ce: “Ina kira ga al’ummar Musulmai su yada hakuri, kauna, da zaman lafiya da juna tsakanin mutane masu banbancin addinai a kasar nan.”

“Na yabawa kokarin Malaman da kuma manyan jami’an gwamnati da su ka halarci wannan zaman.” Buhari ta yi magana kan satar yara inda ta nemi Iyaye su rika nunawa ‘ya ‘ya soyayya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel