Deen Mohammed: Dattijon da sanadiyyarsa sama da mutane dubu 100 suka Musulunta shekaru kadan da komawarsa Musulunci

Deen Mohammed: Dattijon da sanadiyyarsa sama da mutane dubu 100 suka Musulunta shekaru kadan da komawarsa Musulunci

- Ba sabon abu bane idan aka ce Musulunci ne addini mafi habaka a duniya

- Shaikh mutum ne da aka haifa a addinin Hindu amma soyayyarsa ga addinin Musulunci ta sa ya Musulunta

- Bayan Musuluntarsa kuwa ya fada kiran mutane addinin Allah inda yayi nasarar Musuluntar da mutane 108,000

Musulunci ne addinin da yafi kowanne addini yaduwa a doron kasa, wannan ba sabon abu bane. Tun bayan saukar da Al-Qur'ani, shine ya kasance abinda ke taimako tare da nuna hanya ga al'ummar Musulmai.

Musulmai da yawa sun taka rawar gani wajen habaka addinin Musulunci. Tun shekarar 1400 bayan hijira, mutane sun kama hanyar da'awah baya ga bautar Allah.

Malamai da masu kira zuwa ga addinin sun shiga tasku da yawa sakamakon kiran mabiya wasu addinan zuwa Musulunci. Allah ya saka musu da mafificiyar Aljannarsa.

Daya daga cikin masu kiran mutane zuwa ga addinin Allah shine, Deen Mohammed Shaikh, wanda shima Musulunta yayi. Shi kadai ya jawo mutane 108,000 zuwa ga addinin Musulunci.

An haife shi a shekarar 1942 inda ya taso yana bin addinin Hindu a Badin, Sinkh na kasar Pakistan. Ya koma Musulunci ne a shekarar 1989 shi da wani kawunsa. Tun daga nan ya dage da kiran mutane zuwa addinin Allah.

Shi ne shugaban masalallacjn Jami'a Masjid Allah Wali da makarantar koyar da Al-Qur'ani na Aisha Taleemul Qur'an.

Ya fara tsunduma son Musulunci ne tun yana karami inda yake karantasa a sirrance saboda tsoro. Son Musuluncin sa ya cigaba da shiga ransa a hankali kuma ya fusata iyayensa mabiya addinin Hindu.

KU KARANTA: Babbar magana: Mahaifina da kanshi yake duba budurcina ya tabbatar da babu matsala - Jaruma Halima Abubakar

Deen Muhammad ya ce: "Ina matukar kaunar addinin Musulunci, karatun Al-Qur'ani yasa na gano cewa gumaka 360 da muke bautawa basu da amfani a gareni."

Mahaifiyarsa ta hanzarta yi masa aure gudun komawarsa Musulunci, a tunaninta hakan zai janye hankalinsa.

Shaikh ya auri 'yar addinin Hindu amma bai daina son Musulunci ba. Bayan wani dogon lokaci, sai ya yanke shawarar Musulunta. Iyayensa da 'yan uwansa sun juya masa baya banda wani kawunsa da suke da ra'ayi daya, inda suka karbi kalmar shahada tare a shekarar 1989.

Ya samo wani Malami mai suna Muhammad Jangsi wanda ya koya masa Qur'ani da Hadisi.

Ya fara kiran mutane zuwa ga addinin musulunci ne tun daga gida, dangi da kuma al'ummar unguwarsu, yanzu haka dai Deen Muhammad ya jawo mutane 108,000 zuwa musulunci.

Musulmai masu kudi ne suka dau nauyin kiran mutanen da yake zuwa addinin Islama. Sun yi kokarin bashi kudi don amfanin kansa amma yaki yarda ya karba, sai dai ya bukaci da a samawa sabbin mutanen da suka shiga Musulunci aiyukan yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel