Tsarin wutan lantarkin kasashen ECOWAS ya kusa fara aiki a Afrika

Tsarin wutan lantarkin kasashen ECOWAS ya kusa fara aiki a Afrika

Mun ji cewa kungiyar ECOWAS ta kasashen Afrika ta Yamma za ta dabbaka wani shiri na wutar lantarki na Dala biliyan 36.4, a kudin Najeriya wadannan kudi sun haura Naira tiriliyan 13.2.

Za a kawo wannan tsari ne domin inganta wutar lantarkin Yankin na Yammacin Afrika. Wannan aiki zai fara ne daga shekarar nan ta 2019 zuwa 2033 kamar yadda rahotanni su ka bayyana mana.

Masana harkar wuta sun bayyana cewa dole Najeriya ta bunkasa karfin wutar lantarkinta idan har ta na so ayi da iya ita wajen wannan shiri da zai taimaki kasuwan wutan shiyyar Nahiyyar ta Afrika.

Farashin wutan Najeriya ya na cikin mafi karanci a Yankin Afrika don haka ake ganin kasar za ta samu makudan kudi idan har ta rika saida wuta zuwa ga makwabtanta na kusa da ke cikin Nahiyar.

A wajen wani babban taro da kungiyar wuta na WAAP ta kasashen Afrika ta Yamma ta shirya a Garin Abuja, Ministan lantarki, Injiniya Sale Mamman, ya bayyana cewa Najeriya ta na bakin kokarinta.

KU KARANTA: Buhari zai samar da wutar lantarki mai nagarta a Najeriya

Sale Mamman ta bakin karamin Minista, Goddy Agba ya bada sanarwar cewa gwamnatin Najeriya ta na kara kawo wasu ayyukan wuta domin cin moriyar tsarin ECOWAS da za a shigo da shi.

Mista Goddy Jeddy-Agba, ya kaddamar da sabon layin wutan da aka jawo daga tashar lantarkin Kainji a jihar Neja zuwa kasashen Jamhuriyar Nijar, Togo, Burkina Faso a madadin gwamnatin Najeriya.

Jeddy-Agba ya ce wanan ya na cikin shirin da aka amince da shi tun lokacin da aka yi wani taron ECOWAS a Disamban 2018. Shugabannin kasashen ECOWAS ne su ka hadu, su ka yi na’am da tsarin.

Karamin Ministan kasar ya ke cewa dabbaka wannan tsari ya na bukatar kulawa da sa ido. Za a kammala wasu ayyukan wutan da ake yi a Najeriya ne a 2021 domin amfana da tsarin Nahiyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel