Su wanene wadanda aka tsige daga aiki a fadar Shugaban kasa

Su wanene wadanda aka tsige daga aiki a fadar Shugaban kasa

A cikin makon nan ne aka tabbatar da cewa an sallami wasu daga cikin Hadiman da ke aiki da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Daily Trust ta kawo takaitaccen tarihin wasun su.

1. Ajibola Ajayi

Ajibola Ajayi ‘Diya ce wurin tsohon gwamnan jihar Oyo, Isiaka Abiola Ajimobi. Ajayi ta kasance mai ba mataimakin shugaban kasa shawara kan harkar shari’a bayan ta yi aiki a ofishin BPE.

2. Olumuyiwa Abiodun

Mista Olumuyiwa Abiodun ya na cikin masu ba Farfesa Yemi Osinbajo shawara a game da abin da ya shafi lamarin lantarki tun 2017. Ya yi karatunsa ne a kan fannin fasaha a jami’ar Legas.

3. Ife Adebayo

Ife Adebayo ya soma aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa ne tun 2015 a matsayin Mai bada shawara a harkar dabaru da kasuwanci. Adebayo ya yi karatun Digirinsa na biyu ne a Landan.

4. Forri Samson Banu

Bayan sake rantsar da shugaban kasa Buhari da Yemi Osinbajo ne aka nada Samson Banu a matsayin Mai bada shawara kan sha’anin kasuwanci. Banu Lauya ne wanda ya yi aiki da CPC.

5. Edirin Akemu

Ita ma Akemu ta na cikin masu aiki da Osinbajo wajen inganta sha’anin kasuwanci da masanantu da zuba jari. Ta yi aiki da Minista Okechukwu Enelamah kuma ta karanta ilmin tattalin arziki.

6. Imeh Okon

Okon ta soma aiki ne da hukumar BPE tun 2002, kuma ta yi aiki da kungiyar USAID ta Amurka. Okon ce mai ba Osinbajo shawara a kana bin da ya shafi gina-ginen abubuwan more rayuwa.

7. Arukaino Umukoro,

Umukoro ya na aiki ne a matsayin Mai bada shawara a kan harkokin Neja-Delta kafin a tsige sa. Kafin yanzu ya yi aiki da Jaridar Punch kuma ya na da Digirgir a kan yada labarai a kasar waje.

KU KARANTA: NCC za ta magance matsalar wawurar ‘Data’ a Najeriya – Minista

8. Ilsa Ibilola Essien

Ila Essien ta taimaka wajen harkar ciyar da ‘yan makaranta da ake yi. Ta Essien karanci ilmin kasuwanci ne da siyasa da shugabanci. Essien Hadima ce a kan yada labarai kafin a sallame ya.

9. Morakinyo “Mo” Beckley

A Agustan shekarar bana ne aka nada Mo Beckley a matsayin Hadimin mataimakin shugaban kasa kan harkar na’urorin lantarki. Ya yi karatu a Jami’ar Essex kamar Takwarasa Ajibola Ajayi.

10. Yusuf Ali

Dr. Ali kwararre ne a harkar wutar lantarki kuma ya yi karatu ne a Makarantun Wolfson, da Manchester da kuma Cambridge. Ya yi aiki na kusan watanni biyu kenan sai aka sallame sa.

11. Babajide Awolowo

Babajide jika ne wurin Marigayi Obafemi Awolowo. Tun 2005 ya ke aiki da kamfanin Conoil PLC. Jide ya yi karatu a jami’ar Dundee kuma ya kasance mai bada shawara a harkar mai da gas.

12. Akin Soetan

Soetan ya na taimakawa Osinbajo a kan harkar tattalin arziki tun Satumban bana. Ya na Digirin Masters akalla uku a fannin harkokin ketare, da kasuwanci da sauransu a jami’o’i da-dama.

13. Dolapo Bright

A Yunin 2019 aka nada Bright a matsayin Mai bada shawara a wajen cigaban harkar gona. Ya yi aiki a kwamitin tattalin arziki tun 2016. Bright ya yi karatu ne a Jami’ar Obafemi Awolowo.

14. Edobor Iyamu

Kamar dai Arukaino Umukoro, shi ma Edobor Iyamu ya na aiki ne a ofishin mataimakin shugaban kasar a kan harkokin Neja-Delta. Iyamu ya taba zama Hadimi a Majalisa kuma fasto ne a coci.

15. Bala Mohammed Liman

Tsohon Kwamishinan tattali da kasafin kudin na jihar Neja ya fara aiki ne da Osinbajo a bana. Liman wanda ya san tattalin arziki da aikin banki ya na bada shawara ne a kan wannan harkar.

16. Lanre Osibona

A Mayun 2015 aka nada Osibona a matsayin Mai bada shawara wajen harkokin ICT na zamani. Kafin nan ya yi aiki da Yemi Osinbajo a lokacin yakin neman zaben shekarar 2015 a APC.

17. Gambo Manzo

Gambo Manzo Matashi ne da ke ofishin mataimakin shugaban kasar kuma ya ke bada shawara a kan harkar siyasa. Ainihinsa mutumin jihar Gombe ne kuma ya yi aiki a gwamnatin jihar Legas.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel