Waiwaye: Yadda Obasanjo ya kori Garba Shehu da sauran hadiman Atiku 7 a shekarar 2006

Waiwaye: Yadda Obasanjo ya kori Garba Shehu da sauran hadiman Atiku 7 a shekarar 2006

Har yanzu jama'a na cigaba da cece-kuce da tofa albarkacin bakinsu a kan sallamar hadiman mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi.

Batun sallamar hadiman daga aiki na zuwa ne a daidai lokacin da jama'a ke yada jita-jitar cewa ana kokarin rage wa Osinabjo karfin da yake da shi a gwamnati saboda an samu wata 'yar baraka a tsakaninsa da shugaba Buhari.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Buhari n ya bayar da umarnin a sallami hadiman 35 daga cikin fiye da hadimai 80 da Osinbajo ke da su.

A ranar Laraba da ta gabata ne ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya aika wa hadiman takardun sallama daga aiki. Kazalika, wasu rahotannin sun bayyana cewa tuni aka kwace shaidar shiga fadar shugaban kasa daga hannun hadiman da aka sallama daga aiki.

DUBA WANNAN: Manyan masu kudin duniya 5 da basu kammala karatun sakandire ba

Sai dai, a yayin da jama'a ke cigaba da tattauna wannan batu, wasu kafafen yada labarai sun yi 'waiwaye' da Hausawa ke cewa 'adon tafiya' domin tuna yadda tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya sallami wasu hadiman tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, a shekarar 2006.

Daga cikin hadiman Atiku da Obasanjo ya sallama daga aiki a wancan lokacin akwai Malam Garba Shehu wanda a wancan lokacin lokacin ke zaman mai taimaka wa Atiku a bangaren yada labarai. Malam Garba Shehu shine kakakin shugaba Buhari a yanzu.

Sauran hadiman Atiku da Obasanjo ya sallama daga bakin aiki sun hada Yima Sen, Tokunbo Abiola, Dakta A. Ardo, Mista Natt Yaduma, Dakta Ajuji Ahmed da Phi Agbase.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel