Dalilin da yasa hukumar kwastam ta hana kai man fetur garuruwa kusa da iyakoki

Dalilin da yasa hukumar kwastam ta hana kai man fetur garuruwa kusa da iyakoki

Hukumar kwastam ta kasa ta hana kai man fetur garuruwan da ke da nisan kilomita 20 tsakaninsu da iyakokin kasar nan. Bincike ya nuna cewa, garuruwan kusa da iyakokin Najeriya ne suka tsunduma cikin wannan halin na kaka ni kayi.

Akwai garuruwan da ke da iyakoki da kasar Chadi, Niger da Kamaru wadanda wannan abin ya shafa. Ba garuruwa ba, hatta kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta kasa ta nuna damuwarta kan wannan cigaban.

Lauya mai rajin kare hakkin dan adam, Femi Falana yace, hukumar kwastam ta kasa bata da dama ko hurumin bada wannan dokar.

Mai magana da yawun hukumar kwastam ta kasa, Mr Joseph Attah, ya sanar da jaridar The Nation cewa, an bada wannan dokar ne don shawo kan matsalar sumogal din man fetur zuwa kasashen da ke da makwaftaka da Najeriya.

DUBA WANNAN: Hazikan lauyoyin da suka zama SAN da kananan shekaru a Najeriya

Kamar yadda yace, a rufe iyakokin kasar nan da hukumar kwastam tayi daga watan Augusta, ta gano cewa akwai wasu gidajen mai da ke ta yunkurin fitar da man fetur din zuwa kasashen da suke makwaftaka da Najeriya.

Ya kara da cewa, "Takarda tazo mana ne da umarnin mu hana hakan, mu kuma aikinmu ne tabbatar da dokar gwamnati,"

Shugaban kungiyar 'yan kasuwar man fetur, Alhaji Abubakar Maigandi, ya sanar da wakilin jaridar The Nation cewa, hakan zai kara matsi da tsanani ne kawai ga garuruwan da ke kusa da iyakokin kasar nan.

Ya kara da cewa, tabbatar da dokar zai durkusar da 'yan kasuwar da suke da lasisin DPR na siyar da man fetur a yankin.

Ya shawarci hukumar kwastam ta kasa da ta canza salo wajen hana sumogal din a maimakon tsunduma wasu marasa hannu a lamarin cikin halin matsi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel