Firgici: Jirgin sama ya fara hayaki bayan mintuna 10 da tashinsa

Firgici: Jirgin sama ya fara hayaki bayan mintuna 10 da tashinsa

- Hankulan jama'ar sun tashi a yammacin jiya yayin da gobara ta tashi cikin jirgin kamfanin Azman da ya tashi daga Legas zuwa Abuja

- Mintoci goma bayan tashin jirgin, matukin shi ya koma filin sauka da tashin jiragen bayan da gobara ta tashi a bayin jirgin

- An gano cewa, wata fasinja ce ta sha 'shisha' a bayin jirgin, mintoci biyar bayan wutar ta tashi a bayin

Hankula sun tashi jiya yayin da jirgin sama mai lamba rijista JQ2324 da ya tashi daga Legas zuwa Abuja ya fara hayaki a sama, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An gano cewa, jirgin na kamfanin Azman na dauke da fasinjoji 120 ne kuma dole ce tasa ya koma filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammed dake Legas.

Wata fasinja mace ce aka ce ta shiga bayin jirgin inda ta sha shisha. Hakan kuwa ya kawo gobara a bayin jirgin wanda ya kawo tashin hankula.

DUBA WANNAN: Korar hadiman Osinbajo 35: Kakakin mataimakin shugaban kasa ya karyata batun

Daya daga cikin fasinjojin yace: "Fasinjar da aka kama a bayin tana shan shisha an dakatar da ita ne inda aka sanar da ita ba a busa hayaki a jirgi. Amma mintuna basu wuce biyar ba bayan nan hayaki ya tashi daga bayin, abinda yasa matukin jirgin ya juya akalarsa don komawa filin jirgin,"

Matukin jirgin ya koma filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas bayan yunkurin kashe wutar da aka yi ya tashi a tutar babu. Amma kuma jirgin ya sauka lafiya lau inda motar kashe gobara ta isa wajen don kashe gobarar.

Tuni aka cafke budurwar kuma aka mikata ga jami'an 'yan sanda. Matukin jirgin ya bukaci da a kara duba jirgin bayan saukarsu ko zasu iya kara tashi.

A cikin fasinjojin da ke jirgin harda mamallakin kamfanin Payporte, Eyo Bassey.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan filin jirgi, Joseph Alabi, yayi alkawarin binciko lamarin tare da kiran wakilin jaridar Daily Trust

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164