Gidan yari na shekaru 14 idan Malami ya rungumi, sunbanci ‘Daliba - Majalisa
A Ranar Laraba Majalisar dattawa ta fara tafka muhawara game da kudirin da ke kokarin kafa hukuncin dauri har na tsawon shekaru goma sha hudu ga Malamin jami’ar da ya taba ‘Daliba.
Kamar yadda mu ka samu labari daga a jiya Laraba, dokar za ta yi aiki a kan duk Malamin da aka samu ya taba, runguma, ko damke mama ko kwankwaso ko kutiri ko wani sashe na jikin ‘Daliba.
Mai taimakawa shugaban majalisar dattawa wajen hulda da Manema labarai, Ezrel Tabiowo, shi ne ya fitar da jawabi a Ranar 6 ga Watan Nuwamba inda ya ce kudirin ya haura matakin farko.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, shi ne ya kawo wannan kudiri. wanda zai haramta lalatar da ake yi da ‘Dalibai a manyan makarantun gaba da Sakandare da karfin tsiya.
Wannan kudiri ya zo dauke da sashe 27, ya kuma tanadi daurin shekaru biyar zuwa goma sha hudu ga duk ma’aikacin jami’ar da aka samu ya tilasta kwanciya da ‘Daliba ko makamancin haka.
KU KARANTA: Ana zargin wani Inyamuri da sace Bahaushiya da dirka mata ciki
Kudirin bai bada wata dama ta biyan beli domin kwatar kai a gaban kuliya ba. Duk Malamin da ke koyarwa da aka samu ya tara ko ya bukaci yin hakan daga ‘Daliba zai gamu da fushin shari’a.
Haka zalika dokar idan har ta samu karbuwa za ta yi aiki a kan masu yi wa ‘Dalibai barazana ko kuma jefa su cikin wani hali a dalilin bukatar kwanciya da su. Yanzu dai maganar ta fara nisa.
Wannan doka ta haramta sumbunta, ko damka, shafa, runguma, tsirar mace a mama ko gashi ko labba ko kutirinta da sauran duk wani sashe na jiki kamar yadda Ezrel Tabiowo, ya bayyana jiya.
A kudirin da Sanatan ya gabatar a zauren majalisa, har wanda aka samu da laifin aika sakonnin bidiyon batsa ko hotuna tsirara ga ‘Dalibai zai shiga cikin sahun masu lalata da yaran makaranta.
Wannan kudiri ya haramta yin ba’a ko kallon kurilla ko ihu a game da siffar ‘Daliba yayin da ta ke tafiya. Kudirin ya tanadi hukunci ga ‘Daliban da su ka yi wa Malamai sharri da kagen nemansu.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng