Mahaifiyar Jonathan ta yi amanna da dan takarar gwamnan APC a zaben Bayelsa
Eunice, mahaifiyar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ta yi amanna da dan takarar neman kujerar gwamnan jihar Bayelsa a karkashin inuwsar jam'iyyar APC, Cif David Lyon, a zaben da za a gudanar ranar 16 ga watan Nuwamba.
Mahaifiyar tsohon shugaban kasar ta sanya wa Lyon albarka a garin Otuoke da ke karkashin karamar hukumar Ogbia, yayin da dan takarar da tawagarsa suka ziyarci mazabun kananan hukumar Ogbia domin yakin neman zabe.
Wasu manyan masu fada a ji a karamar hukumar Ogbia da kuma wasu na hannun damar Jonathan irinsu Cif Robert Enogha, wanda ya bar gwamnati kwanan nan kuma ya koma APC, sune suka jagoranci Lyon zuwa gidan mahaifiyar Jonathan.
Dan takarar na jam'iyyar APC ya durkusa ya gaisar da mahaifiyar Jonathan sannan ya nemi ta albarkace shi tare da yi masa addu'a.
DUBA WANNAN: Makiyaya sun harbi dan sanda da manomi, sun kone kauye guda a jihar Jigawa
Mahaifiyar Jonathan, wacce ta yi magana a cikin harshen Ogbia cikin murmushi da annashuwa, ta yi ruwan addu'o'in samun nasara ga Cif Lyon a zaben mai zuwa..
Da yake fassara kalamanta cikin harshen Turanci, wani na hannun damar Jonathan mai suna Wisdom Ikuli, ya ce dattijuwar ta bayyana cewa, "David da ne a wurina, a saboda haka, amadadin dukkan iyalina, na saka maka albarka, Allah yana son yin amfani da kai domin kawo jihar Bayelsa canji."
Da yake kara tabbatar da goyon bayan jama'ar yankin ga dan takarar, Ikuli ya ce: "mutanen Otuoke sun yi magana kuma sun nuna wa duniya ta gani inda suka karkata. Sun sanar da gwamnan jihar Bayelsa mai jiran gado, Cif David Lyon, cewa sun albarkace shi.
"Domin mu tabbatar masa da cewa ya samu goyon bayanmu, shine muka kai shi gaban mahifiyar mu, Eunice Jonathan, mahaifiyar tsohon shugaban kasa, GoodLuck Jonathan, wacce ta kara yi masa ruwan addu'o'i da fatan alheri."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng