Kyawun alkawari cikawa: Gbajabiamila ya dauki nauyin jaririya mara lafiya, ya saya mata gida a Katsina

Kyawun alkawari cikawa: Gbajabiamila ya dauki nauyin jaririya mara lafiya, ya saya mata gida a Katsina

Kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya dauki nauyin kulawa da wata jaririya mai suna Halima Abubakar da aka haifa da wata matsalar rashin lafiya a jahar Katsina, inda ya biya mata kudin asibiti a babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito a kwanakin baya ne Gbajabiamila ya hadu da wannan jaririya a sansanin yan gudun hijira yayin wata ziyara daya kai jahar Katsina, inda ya yi alkawarin daukan nauyin jaririyar, tare da bata kulawar daya kamata.

KU KARANTA: Majalisar dokokin jaha ta amince da nadin kwamishinoni 23 a gwamnatin Adamawa

Mashawarcin Gbajabiamila a kan harkar yan gudun hijira, Hamza Baba, ya bayyana cewa iyayen jaririyar, Abubakar da Nafisa sun fito ne daga kauyen Wagini dake cikin karamar hukumar Batsari a dalilin ayyukan yan bindiga da suka addabi yankin.

Hamza yace: “Ina farin cikin sanarwa da cewa jaririya Halima, mahaifiyarta Nafisa da mahaifinta Abubakar da sauran yan uwanta a yanzu haka suna cikin farin ciki da kwanciyar hankali a wani gida ciki biyu da muka kawatashi da kayan alatu a cikin garin Katsina.

“Kaakakin majalisa Gbajabiamila ya basu isashshen kayan abinci, da kayan sawa, sa’annan ya fara shirye shiryen daukan nauyin mahaifinta da mahaifiyarta domin horas dasu sana’ar da su dogara da kansu da ita, wannan na daga cikin manufofinsa na inganta rayuwar yan gudun hijira.

“A yanzu mun fara tsare tsaren mayar da yan gudun hijiran zuwa garuruwansu, inda muka fara da kai ziyarar ban girma zuwa ga hakimin Batsari, Alh Muazu Tukur da hakimin Wagini Dikko Muazu, sa’annan mun gana da jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Katsina, da kuma jami’an karamar hukumar Batsari a karkashin jagorancin matar Ciyaman, Hajia Ummah.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya yi wata ganawar sirri tare da dukkanin masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro a jahar Kaduna, inda suka goga gemu da gemu tare da musayar ra’ayi a kan yadda za’a shawo kan matsalar tsaro a Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel