APC ta lallasa PDP a Sokoto yayinda kotun daukaka kara ta jaddada zaben Wamakko

APC ta lallasa PDP a Sokoto yayinda kotun daukaka kara ta jaddada zaben Wamakko

Kotun daukaka kara dake zama a Sokoto a ranar Litinin, 4 ga watan Oktoba ta tabbatar da zaben sanata Aliyu Wamakko a matsayin sanata mai wakiltan Sokoto ta tsakiya, ta kuma yi watsi da karar da Sanata Ahmad Maccido ya daukaka akan hukuncin kotun zaben majalisar dokokin tarayya da na jiha.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa a ranar 6 ga watan Satumba ne kotun zaben ta yi watsi da karar da Maccido na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya shigar, inda yake kalubalantar zaben Wamakko na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin kotun zaben, sai Maccido ya daukaka kara inda ya kalubalanci hukuncin kotun zaben.

A hukuncin kwamitin mutum uku karkashin jagorancin Justis Ibrahim Saulawa wanda Justis Hamma Akawu ya karanto, ya bayyana cewa kotun daukaka karar ta riki hukuncin kotun zaben.

NAN ya ruwaito cewa kwamitin ya kuma soke karar da Aminu Shagari da Kabiru Achida na PDP suka shigar inda suke kalubalantar hukuncin kotun zabe kan Abubakar Yabo da Almustapha Rabah na APC.

KU KARANTA KUMA: An zo wurin: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan karar da PDP ta daukaka a kan El-Rufa'i

Shagari da Achida sun yi takarar zaben 2019 a mazabun Yabo/Shagari da Rabah/Wurno duk a karkashin PDP.

Da yake karanto hukuncin Justis Saulawa ya ce kotun bata da hurumin sauraron lamarin, domin wa'adin kwanaki 60 da kotun ke da shi na sauraron lamarin ya cika a ranar 2 ga watan Nuwamba da 3 ga watan Nuwamba.

Kotun ta kuma yi watsi da karar da Alhaji Sa'idu Na Bunkari na APC ya daukaka inda ya ke kalubalantar zaben Alhaji Mani Maishinku na PDP a mazabar Binji/Silame da ke jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel