An karrama jaruma Fati Washa a Birtaniya

An karrama jaruma Fati Washa a Birtaniya

Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, Fatima Abdullahi wacce aka fi sani da Fati Washa, ta karbi kyautar gwarzuwar jaruman hausa a wani bikin fina-finan Afirka da aka yi a Birtaniya.

Washa ta amshe kyautar gwarzuwar shekarar ne a taron karrama 'yan Fim da aka yi a ranar Asabar a birnin Landan.

Taron da aka sani da Afro Hollywood Awards, ya shafi karrama tare da jinjinawa jaruman fim din harsunan Najeriya ukun da suka hada da Hasua, Yoruba da Igbo da kuma fannin turanci a sassan nahiyar Afirka.

DUBA WANNAN: 2020: Buhari ya tsayar da ranar bude iyakokin Najeriya

An karrama jaruma Fati Abdullahi washa ne sakamakon rawar da ta taka a Fim mai suna 'Sadauki'.

Jarumar ta doke jarumai Aisha Aliyu Tsamiya ne a Fim din "Jamila" da kuma Halima Yusuf Atete a Fim din "Uwar Gulma".

Jaruma Rahama Sadau ta wallafa bidiyon jaruma Fati Washa a shafinta na Instagram, yayin da Fatin ke karbar kyautar. Rahama ta nuna farincikinta tare yiwa jarumar fatan alkhairi.

Itama jaruma Fati Washan ta wallafa bidiyon a shafinta na Instagram inda take bayyana farincikinta. Jarumar tace ta sadaukar da kyautar ga masoyanta tare da godiya garesu.

Wannan ne karo na 23 da ake gudanar da bikin karrama jaruman fina-finan wanda Jaridar African Voice da ke Birtaniya tare da tallafin gudauniyar Esther Ajayi da Ned Nwoko ke daukar nauyi.

Mashiryan bikin a Birtaniya sun bayyana cewa sama da fina-finai 500 ne daga nahiyar Afirka ke shiga gasar da aka fara tun 1996.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng