Ni da kudi na nake yin harkar fim ba 'yar ku ci ku bani bace - Jaruma Safna Aliyu ta yi martani mai zafi

Ni da kudi na nake yin harkar fim ba 'yar ku ci ku bani bace - Jaruma Safna Aliyu ta yi martani mai zafi

- Jaruma Safna Aliyu Maru tayi martani ga masu cewa ta kare mata an daina yayin ta a harkar fim

- Jarumar ta ce sam ba haka lamarin yake ba, yanzu ta mayar da hankalinta a harkar kasuwa ne shine yasa bata fitowa a fim

- Jarumar ta kara da cewa kowa ya san ita furodusa ce, kuma tana amfani da kudinta ne wajen shirya fim, saboda haka har yanzu ana yayin ta

Daya daga cikin jarumai mata da tauraruwar su ta haska a baya mai suna Safna Aliyu wacce a yanzu ta dauki mai tsawo ba tare da an ganta a cikin harkar fim ba, jarumar ta bayyana rashin fitowarta a fim a matsayin wani abu da ya shafi al'amari na kanta ba wai don an daina yayin ta bane ko kuma an daina harka da ita a fim bane.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin da tayi hira da wakilin jaridar dimokaradiyya Mukhtar Yakubu kan rashin ganinta da aka yi a harkar fim na tsawon lokaci.

Jarumar ta ce: "Gaskiya na dan dauki lokaci bana harkar fim, kuma harma wasu na ganin kamar ko an daina yayi na ne, gaskiyar magana ba haka bane, domin kuwa duk wanda ya san Safna Aliyu Maru a harkar fim ya san ba a daina yayi na ba, har yanzu ana yayi na kawai dai a yanzu na kara fadada harkoki na ne na kasuwanci," in ji ta.

KU KARANTA: Michael Jackson: Duk da cewa ya shekara 10 da mutuwa amma har yanzu shine tauraron mawaka da yafi kowa daukar albashi a shekarar 2019

Ta cigaba da cewa: "Dan haka sai ya kasance bana samun lokaci sosai saboda tafiye-tafiye da nake yi na harkar kasuwanci, don a yanzu na fi maida hankalina wajen kasuwanci, yanzu ina fita waje na sayo kayayyaki kamar su atamfofi, yadika da takalma, hakan yasa na mayar da hankalina akan wannan harkar domin na samu na gina ta."

Sannan ta ce: "Su masu ganin kamar ta kare mini, sam abin ba haka yake ba, saboda ni da kudi na nake yin harkar fim, kowa ya san cewa ni furodusa ce, na shirya fina-finai da yawa da kudi na, kuma har yanzu ina da kudi da yawa a kasuwa, dan haka ai bata kare mini ba," in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel