Jarumi Sallau na 'Dadin Kowa' ya aikawa da Adam A Zango budaddiyar wasika

Jarumi Sallau na 'Dadin Kowa' ya aikawa da Adam A Zango budaddiyar wasika

- Bayan abin alkhairin da jarumi Adam A Zango yayi na daukar dalibai karatu

- Yanzu dai haka mutane na ta faman sanya masa albarka akan wannan alkhairi da yayi

- Hakan ya saka shima jarumin fim din 'Dadin Kowa' Sallau ya nuna cewa shima baza a barshi a baya ba

Bayan abin alkhairin da jarumi Adam A Zango yayi na daukar nauyin dalibai sama da guda dari domin su yi karatu a wata babbar makaranta dake garin Zariya, mutane da dama suna sanya albarka akan irin wannan abin alkhari da jarumin yayi, inda suke shi masa albarka da kuma fatan alkhari.

Wannan dalili ne ya sanya jarumin barkwancin nan na fim din 'Dadin Kowa' wanda aka fi sani da Sallau ya fito ya tofa albarkacin bakin sa ya kuma bayar da shawarwari ga jarumi Adam A Zango. Ga dai abinda jarumin ya ce a wani sabon bidiyo da ya fitar:

"Assalamu Alaikum Warahamatullahi Ta'ala Wa Barakatuhu, Adam Zango Allah ya saka maka da alkhairi akan wannan abin alkhairi da kayi, ubangiji Allah ya biya ka ya kuma saka maka a mizaninka.

KU KARANTA: Tashin hankali: Sacewa wata Bafulatana tunkiya ya saka ta sha alwashin kashe wanda ya dauke mata dabba

"Hassada dole ne ayi maka hassada saboda ko Annabi da aka aiko anyi masa hassada, saboda haka kayi hakuri kuma ka duba su waye suke yi maka hassadar sun kai suyi maka hassadar ko basu kai ba.

"Haka zaka cigaba da zama da munafukai, ko Annabi sai da ya sha fama da munafukai, har Surah sukutum aka saukar saboda munafukai, da za a daina munafurci da ba a saukar da wannan surar ba.

"Wannan abu da kayi na alkhairi Allah yasa kayi dubun dubatarsa, Allah kuma ya bamu iko mu biyo bayanka."

Idan ba a manta ba makonnin da suka gabata ne jarumi Adam A Zango ya dauki nauyin karatun wasu dalibai 101, inda ya biya musu kudi sama da miliyan arba'in da shida (N46m).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel