Fadar Shugaban kasa: Buhari ya amince da tayin kasar Saudiyya na kafa Majalisa da Najeriya

Fadar Shugaban kasa: Buhari ya amince da tayin kasar Saudiyya na kafa Majalisa da Najeriya

A Yau, 31 ga Watan Oktoba, 2019, Fadar shugaban kasa ta fitar da jawabi game da nasarorin da aka samu a ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai zuwa kasar Saudi Arabiya.

Yanzu haka shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kada wata majalisa ta Saudi da kasar Najeriya. Wannan majalisa za ta taimaka wajen habaka alakar kasuwancin da ke tsakanin kasashen.

Fadar shugaban kasar tace wannan ce babbar nasara da aka samu a zaman shugaba Muhammadu Buhari da Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman a wajen taron da aka shirya.

Kamar yadda fadar shugaban kasar ta fitar da jawabi, ya kamata ace ne shugabannin sun hadu a ofishin Yarima Mohammed Salman. Amma a karshe Yariman ya zo har otel din shugaba Najeriyar.

Girmamawa ta sa 'Dan Salman ya zo otel din da shugaba Buhari ya tare na The Ritz Carlton da ke Birnin Riyadh domin su tattauna yadda za a kafa majalisar da za ta bunkasa tattali da tsaron Najeriya.

KU KARANTA: ISIL ta yi sabon shugaba bayan kashe Al-Baghdadi

Wannan majalisa da za a kafa cikin wata biyu, za ta kunshi jami’an gwamnati da ‘yan kasuwar kasashen. Za a maida hankali ne wajen cigaban tattalin arziki, da harkar kasuwanci da sha’anin tsaro.

Za a rika zama ne sau biyu a shekara a wannan majalisa. Haka zalika shugabannin kasashen za su zauna sau guda a duk shekara domin ganin inda aka kwana. Wannan zai taimaka wajen inganta tafiyar.

Shugaban Najeriya ya yabawa Saudi da ta zabi ta hada-kai da Najeriya inda ya fadawa Yariman kasar cewa akwai gogaggun Matasa a Najeriya da za su amfana da wannan, tare da jan hankali kan tsaro.

Mai jiran gadon na Saudi ya fadawa Buhari cewa Najeriya ta na iya shiga cikin manyan kasashe 20 na Duniya. Salman ya kuma fadi shirinsu na sa kudi a Najeriya kamar yadda su ka yi a Indiya da Fakistan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel