'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 46 a Kebbi, sun dakile N1.5m biyan kudin fansa

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 46 a Kebbi, sun dakile N1.5m biyan kudin fansa

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kebbi ta dakile biyan miliyan N1.5 a matsayin kudin fansa tare da kama wasu mutane 46 da suke zargin masu garkuwa da mutane ne tare da wasu masu kai musu bayanai.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Garba M. Danjuma, shine wanda ya sanar da hakan yayin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai a hedikwatar 'yan sandan jihar Kebbi da ke Birnin Kebbi.

Mista Danjuma ya shaida wa maneman labarai cewa wani mutum mai suna Alhaji Abubakar Chindo, mazaunin karamar hukumar Bunza, shine ya fara sanar da rundunar 'yan sanda cewa an kira shi a waya tare da yi masa barazanar cewa za a sace shi idan bai biya miliyan N1.5 ba.

"Bayan ya shigar da korafi ne sai jami'an mu suka fara bincike, lamarin da ya kai ga an kama wani mutum mai suna Muhammed Danbawa da abokinsa mai suna Abubakar Abdullahi," a cewar kwamishinan.

Kwamishin ya bayyana cewa mutanen biyu sun bawa rundunar 'yan sanda hadin kai a binciken da take gudanarwa, lamarin da ya kai ga rundunar ta kama wasu mutane; Aliyu Bala, Zayyanu Basiru, Muhammed Sarkin Fulani da Ibrahim Dankawo, dukkansu mazauna karamar hukumar Shanga. Ana zarginsu da taimaka wa masu garkuwa da mutane da bayanai da kuma karbar kudin fansa.

DUBA WANNAN: SERAP ta rubuta wa Trump wasikar neman ya haramta wa gwamnoni 7 shiga Amurka

Ya kara da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumarsu da laifin hada kai da 'yan ta'adda da kuma goyon bayan garkuwa da mutane.

Mista Danjuma ya bayyana cewa sun kama sauran masu garkuwa da mutanen ne a kauyukan jihar da wasu garuruwa da suka hada da; Fakai, Arewa, Shanga, Birnin Kebbi, Jega, Danko-Wassagu, Zuru, da karamar hukumar Bunza.

A cewar kwamishinan, rundunar 'yan sandan jihar ta kara kama wani dan kungiyar masu garkuwa da mutane mai suna Hussaini Dahiru Labbo, mazaunin kauyen Ingarje a karamar hukumar Jega, wanda kuma shine ake zargin ya jagoranci yin garkuwa da matar wani mutum mai suna Alhaji Saidu Abdullahi.

Ya ce rundunar 'yan sanda za ta gurfanar da masu laifin a gaban kotu da zarar ta kammala bincike domin a zartar da hukunci a kansu.

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 46 a Kebbi, sun dakile N1.5m biyan kudin fansa
'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 46 a Kebbi
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel