Jam’iyyar APC ta yi ma zaben kananan hukumomin jahar Kebbi ‘Cinye du’

Jam’iyyar APC ta yi ma zaben kananan hukumomin jahar Kebbi ‘Cinye du’

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jahar Kebbi, KESIEC ta sanar da jam’iyyar APC mai mulki a jahar ta lashe dukkanin kujerun da aka fafata a zaben kananan hukumomin jahar na ranar 26 ga watan Oktoba.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana shugaban hukumar KESIEC, Alhaji Aliyu Mera ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a Birnin Kebbi a ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin wani hamshakin mai taimakon jama’a a Katsina

Aliyu Mera ya bayyana cewa: “KESIEC na sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin jahar Kebbi a hukumance, an gudanar da zaben ne a ranar Asabar a mazabu 223 da kananan hukumomi 21, jam’iyyar APC ta samu nasara a dukkanin kananan hukumomi 21. Jam’iyyun PDP da Fresh Party basu tabuka wani abin a zo a gani ba a zaben.”

Sai dai, Mera ya kara da cewa zabe a wasu rumfunan zabe guda biyu dake karamar hukumar Argungu da Dandi bai kammalu ba, “Sai a ranar Asabar 2 ga watan Nuwamba zamu kammalasu.” Inji shi.

Daga karshe Alhaji Mera ya bayyana farin cikinsa duba da yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, sa’annan ya kara da cewa a gaban jami’an tsaro da wakilan jam’iyyun siyasa aka sanar da sakamakon zaben.

A wani labari kuma, a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba ne kotun koli ta yi watsi da karar da Atiku ya shigar gabanta inda yake kalubalantar nasarar da Buhari ya samu a zaben shugaban kasa, tare da kalubalantar hukuncin kotun sauraron koken zaben shugaban kasa da ta tabbatar da nasarar Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng