Innalillahi: Wani mugun likita ya shafawa yara sama da 900 cutar HIV bayan yayi amfani da allura guda daya a kansu

Innalillahi: Wani mugun likita ya shafawa yara sama da 900 cutar HIV bayan yayi amfani da allura guda daya a kansu

- An kama wani tantirin likita da ya shafawa sama da yara 900 cutar kanjamau a kasar Pakistan

- An bayyana cewa likitan yana yin amfani da tsohuwar allura wajen yiwa yaran allura ko karin ruwa

- Haka kuma an bayyana cewa asibitin likitan yafi na kowa araha a fadin garin abinda ya sanya mutane tururuwar zuwa kenan

Sama da yara kanana guda dari tara ne suka kamu da cutar kanjamau sanadiyyar wani dan iskan likita wanda ya dinga amfani da allura guda daya wajen ba su magani a kasar Pakistan.

A farko-farkon shekarar nan dai an ruwaito cewa an samu karuwar matsalar akan kusan mutane dari biyar a garin Ratodero.

Amma yanzu mutane sun karu sun kai kimanin su dubu daya da dari daya a ciki kuma guda dari tara duk yara ne, bayan wani likita mai suna Dr Muzaffar Ghanghro yayi amfani da allura guda akan su duka.

Likitan dai yana karbar kudi mafi araha a fadin garin, hakan ya sanya mutane suke tururuwar zuwa wajen shi.

A yanzu haka dai an gwada kimanin mutane 200,000 a garin, inda masana suke fargabar cewa yaran na iya karuwa, kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Bidiyo: An kama daliban wata sakandare a Najeriya suna lalata a aji

Wani mutumi mai suna Imtiaz Jalbani ya kaiwa likitan 'ya'yanshi har guda shida, inda ya bayyana cewa yaga lokacin da ya dinga sanya hannunshi a cikin kwandon shara yana dauko tsohuwar allura yana yiwa 'ya'yanshi da ita, inda daga baya akan bayyana masa cewa duka sun kamu da cutar kanjamau din.

Hudu daga cikin 'ya'yan nashi duka sun kamu da cutar inda biyu daga cikinsu kuma suka riga suka mutu.

Wasu mutane suma sun bayyana cewa likitan yayi amfani da allura daya wajen sanyawa yara kimanin 50 ruwa.

Yanzu haka dai an kama shi da laifin sakaci da kuma kisan kai bayan wannan lamari ya fito fili.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel