Bidiyo: An kama daliban wata sakandare a Najeriya suna lalata a aji

Bidiyo: An kama daliban wata sakandare a Najeriya suna lalata a aji

- Wani bidiyo da yake ta faman yawo a shafukan sadarwa na yanar gizo ya bayyana yadda wasu dalibai suke lalata da juna a cikin aji

- Wannan bidiyo dai ya nuna yadda daliban suka nuna halin ko in kula ga 'yan uwansu dalibai duk da cewa sun san da cewa suna daukar su a bidiyo

- Duk da dai cewa ba a bayyana ainahin inda wannan lamari ya faru ba, amma wata majiyar ta bayyana cewa wannan lamari ya faru a daya daga cikin makarantun sakandare na Najeriya

Wani bidiyo na wasu da ake tunanin daliban makarantar sakandare ne da aka kama su suna holewa a cikin aji ya yadu a shafukan sada zumunta na zamani.

A yadda bidiyon ya nuna, kowanne daga cikin daliban an nuno shi da budurwar shi sun kama kwana daya a cikin ajin suna ta rungume-rungume ga juna.

A lokacin da aka wallafa wannan bidiyo dai ba a bayyana inda wannan lamari ya faru ba, amma wata majiyar ta bayyana cewa wannan lamari ya faru a daya daga cikin makarantun sakandare na Najeriya ne.

KU KARANTA: Bayan daukar lokaci muna soyayya na gano cewa budurwa ta tantiriyar 'yar iska ce ta zubar da cikin shege har sau biyu - Saurayi ya tona asiri

Duk da cewa ba a bayyana ainahin inda wannan lamari ya faru ba, amma a yadda bidiyon ya bayyana daliban sun sani sarai cewa 'yan uwansu dalibai suna daukar su a bidiyo amma ko su nuna sun damu suka cigaba da lalatar su a cikin ajin.

Yayin da ake fama da matsala ta Malaman jami'a da suke lalata da dalibai a makaranta don su basu maki, sai gashi ana samun irin wannan abu a makarantun sakandare, wannan yasa mutane ke tambayar shin anya lokaci zai zo da za a daina irin wannan abu a kasashen mu na Afrika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel