TY Buratai ya nada sabon Shugaban NDA da wasu manyan mukamai

TY Buratai ya nada sabon Shugaban NDA da wasu manyan mukamai

Shugaban hafsun Sojin kasan Najeriya, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai, ya amince da sauyi da nadin mukaman aikin da su ka shafi wasu Manjo Janar 5 da Birgediya Janar 4 na Najeriya.

Kamar yadda mu ka ji labari daga bakin Mukaddashin Darektan sojojin na hulda da Jama'a, Kanal Sagir Musa, daga cikin Sojojin da aka canzawa wurin aiki akwai Manjo-Janar Jamil Sarham.

Sagir Musa ya bayyana wannan ne a jawabin da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja Ranar 29 ga Watan Oktoba. Manjo-Janar F.O Agugo ya zama sabon GOC na shiyya ta shida da ke Fatakwal.

Tsohon GOC na Fatakwal din watau Manjo-Janar Jamil Sarham shi ne ya zama shugaban makarantar sojoji ta NDA da ke Kaduna. Manjo-Janar I.M Yusuf ya zama Jagoran MNJTF a Chad.

KU KARANTA: Direban mota ya aika Jami'in KAROTA barzahu a Garin Kano

Musa ya ce Manjo-Janar C.O Ude ya bar Hedikwatar MNJTF da ke Garin Ndjamena zuwa cibiyar Nigerian Army Resource ta Abuja. An kuma dauke Manjo-Janar E.N Njoku daga Hedikwatar Soji.

Birgediya-Janar E.J Amadasun zai bar aikinsa a makarantar harkar makamai da ke Kontogora zuwa Barikin Abeokuta inda zai zama Jagora. Birgediya-Janar A.M Adetayo ne ya canje sa a nan.

A wannan sababbin nade-nade, Birgediya-Janar L.M Zakari ya bar kujerar da yake kai a Kwalejin ilmi, kimiyya da fasaha na Sojoji da ke Ilorin, Zakari ya koma Hedikwatar Sojin kasar a Abuja.

Haka zalika Birgediya-Janar E. Ekpenyong ya ajiye aikinsa na kula da makarantar Sojoji da ke Garin Ojo a Legas. Yanzu ya zama Darektan da ke lura da gidan makaman kasa inji Kanal Musa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel