Wata sabuwa: Kotu ta kara kwace kujerar APC a jihar Sokoto

Wata sabuwa: Kotu ta kara kwace kujerar APC a jihar Sokoto

- Kotun daukaka kara ta kwace kujerar wani dan majalisar tarayya na APC

- Dan majalisar tarayyar da abin ya shafa, Alhaji Bala Hassan na wakiltar mazabar tarayya ta Sakkwato ta arewa ne da Sakkwato ta kudu

- Kotun daukaka karar ta bada umarni ga hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da ta yi sabon zabe a cikin kwanaki 90

Zamu iya cewa cikin kwanakin nan, 'yan jam'iyyar APC sun tsinci kansu cikin mawuyacin hali a yawancin shari'un da akeyi. Domin kuwa ana ta maka su da kasa a kotu.

Sabon abinda ya samu jam'iyyar a jihar Sokoto kuwa shine hukuncin kotun daukaka kara da ta umarnin a yi sabon zaben mazabar tarayya ta arewacin Sokoto da Kudancin Sokoto, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Mutuwar mai laifi: Jarumin dan sanda Abba Kyari ya shiga tsaka mai wuya

Idan zamu tuna, Abubakar Abdullahi, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2019, ya daukaka karar hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben da Alhaji Bala Hassan na jam'iyyar APC yayi nasara.

Bayan nazari akan shari'ar ne, Jastis Oho na kotun daukaka kara ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da ta yi sabon zabe a cikin kwanki 90 masu zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel