Dakarun Sojan ruwa sun kwato dabbobi 318 mallakin Fulani daga hannun barayi

Dakarun Sojan ruwa sun kwato dabbobi 318 mallakin Fulani daga hannun barayi

Dakarun rundunar Sojan ruwa ta Najeriya sun samu nasarar kwato shanu guda 318 daga hannun barayin mutane daban daban tare da kama wasu barayin dabbobin guda 5 a yankin karamar hukumar Kachia na jahar Kaduna.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa kwamandan kwalejin kimiyyar makamai na rundunar Sojan ruwa, Commodorw Tanko Pani ne ya bayyana haka yayin da yake mika dabbobin ga shugaban karamar hukumar Kachia a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Hukumar kwastam ta kama sundukai 32 makare da shinkafar kasar waje fal!

Kwamandan yace daga cikin dabbobin akwai shanu guda 267 da awaki 51, ya kara da cewa sun kama dabbobin ne yayin da suka bi sawun wasu gungun barayin shanu bayan sun tarkata shanun daga garin Kujama a ranar 26 ga watan Oktoba.

Kwamanda Pani ya tabbatar da cewa satar shanu, garkuwa da mutane da da kuma hare haren yan bindiga ba wani sabon abu bane a yankin Kachia, amma yace sun samu nasarar rage aukuwar miyagun ayyuka a yankin tun bayan darewarsa mukamin kwamanda a kwalejin.

“Za mu cigaa da bin diddigin miyagu a duk inda suke har sai mun murkushesu, amma dai muna neman gudunmuwar jama’a dasu cigaba da bamu ingantattun bayanan sirri game domin mu yi aikinmu yadda ya kamata.

“Da wannan nake mika ma gwamnatin jahar Kaduna dabbobin nan da barayin shanun guda 5 domin ta dauki matakin daya kamata. Daga karshe a sani rundunar Sojan ruwa za ta cigaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kawar da ayyukan miyagun daga Kaduna.” Inji shi.

A nasa jawabin a yayin da yake karban dabbobin, shugaban karamar hukumar Kachia, Peter Agite ya jinjina ma rundunar Sojan ruwa, sa’annan ya yi alkawarin aiki tare da rundunar da sauran hukumomin tsaron domin tabbatar da tsaro a yankin.

Daga karshe ya yi kira ga duk masu dabbobin da su bayyana kansu domin a basu a binsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel