Kano: Sarkin Karaye ya rushe majalisarsa

Kano: Sarkin Karaye ya rushe majalisarsa

Mai martaba Sarkin Karaye a jihar Kano, Dakta Ibrahim Abubakar II ya rushe majalisar masu rike da sarautun gargajiya na masarautarsa.

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun Jami'in watsa labarai na karamar hukumar Karaye, Mallam Haruna Gunduwawa.

Daily Trust ta ruwaito cewa an gano sarkin ya bayar da umurnin rushe majalisar ne jim kadan bayan taro da ya yi da masu rike da sarautun gargajiya na masarautar masu barin gado a fadarsa a ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: Wani mutum ya 'mutu' ya dawo bayan shekara 30 a Kano

Magajin garin Karaye kuma daya daga cikin manyan masu rike da sarauta a masarautar, Injiniya Shehu Ahmad ya ce rushe majalisar bai shafi mukamman hakimai takwas da ke masarautar ba.

Sarkin na Karaye ya ce masarautarsa za ta fadada sarautun kuma wasu daga cikin masu rike da sarautar za su koma kan sarautarsu yayin da wasu daga cikinsu za su samu karin girma.

A cewar babban mai rike da sarautan, Sarkin ya mika godiyarsa da masu sarautun bisa gudunmawar da suka bayar wurin cigaban masarautar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel