Saudiyya za ta koma Aljannar duniya: Za a shuka bishiyoyi kala-kala har guda miliyan 5 a kasar Saudiyya

Saudiyya za ta koma Aljannar duniya: Za a shuka bishiyoyi kala-kala har guda miliyan 5 a kasar Saudiyya

- Kasar Saudiyya ta sha alwashin shuka bishiyoyi guda miliyan biyar a fadin kasar

- Kasar ta dauki wannan kuduri ne daga yanzu zuwa shekarar 2030 domin kawo canjin yanayi mai inganci a kasar

- Kasar Saudiyya dai tana fama da matsala irin ta kwararowar hamada da matsaloli na hayaki na ababen hawa da dai sauransu

Bishiyoyi da dazuka suna da matukar muhimmanci ga mutane musamman a wannan zamanin da muke ciki da ake ta samun matsala na kwararowar hamada, amfani da sinadarai masu guba, hayakin ababen hawa da dai sauransu. Yanzu haka zafi na kara karuwa a ko ina a fadin duniyar nan saboda karancin bishiyoyi da ake samu.

Wannan matsala da rashin bishiyoyi ke kawowa ya sanya kasar Saudiyya shan alwashin shuka bishiyoyi guda miliyan biyar a fadin kasar daga nan zuwa shekarar 2030. A yadda wata majiya ta bayyana, kasar ta dauki kudurin shuka wadannan bishiyoyin ne ta hanyar amfani da ruwan da ya lalace wanda aka sarrafa.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Kasar Saudiyya ta cire dokar zuwa aikin Hajji da muharrami ga mata

Kasar dai ta dauki wannan kuduri ne domin dawo da yawan bishiyoyi da dazuka a kasar, haka kuma hakan zai saka a samu canjin yanayi mai inganci a fadin kasar, sannan kuma shuka bishiyoyin zai rage matsalar kwararowar hamada, matsalar hayakin ababen hawa da dai sauransu.

Mutane da yawa ba su san cewa yankin kasar Saudiyya a shekarun baya daji ne mai cike da bishiyoyi da koramu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel