2019: A 65, babu ni babu siyasa daga yanzu kuma – Inji Asonya Adokwe

2019: A 65, babu ni babu siyasa daga yanzu kuma – Inji Asonya Adokwe

Mun samu labari dazu cewa Sanata Suleiman Asonya Adokwe ya ajiye siyasa a Najeriya. Hakan na zuwa ne bayan tsohon Sanatan na Nasarawa ya gaza karbe kujerarsa a kotun karar zabe.

Suleiman Asonya Adokwe ya wakilci Nasarawa ta Kudu a majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar PDP. Tsohon gwamnan jihar, Umaru Tanko Al-Makura, shi ne ya tika sa da kasa a bana.

Asonya Adokwe yake cewa: “A shekara 65 a Duniya ba zan iya zuwa ina neman kujerar siyasa ba. Na kai matsayin da zan zama Dattijo, amma tsaya tsakara ba ya cikin lissafin a yanzu kuma.”

Sanatan ya nuna cewa ya amince da shari’ar da kotun ta yi inda aka tabbatar da nasarar Umaru Tanko Al-Makura a matsayin zababben Sanatan Yankin Kudancin Nasarawa a majalisar Dattawa.

KU KARANTA: 2023: Ibo su na harin takarar Shugaban kasa a Najeriya

‘Dan siyasar mai shekaru 65 a Duniya ya bayyana cewa bai da ja da zabin da Ubangiji ya yi a shari’ar da ya daukaka, ganin cewa ya yi aiki a majalisar dattawa na shekaru goma sha biyu.

Sau uku ana zaben Adokwe a matsayin ‘dan majalisa. Sai dai sirri na say a karye a zaben 2019 inda ya sha kashi a hannun gwamna mai-ci a lokacin, Umar Tanko Al-Makura na jam’iyyar APC.

Sanatan na Nasarawa ta Kudu ya shigar da kara a gaban kotu ya na kalubalantar nasarar da APC ta samu. Sanatan bai yi nasara ba, don haka ya daukaka kara, inda a nan ma aka ba APC gaskiya.

A 2007 aka fara zaben Asonya Adokwe a matsayin Sanata inda ya rike manyan kwamitoci da su ka hada da Sojin ruwa da man fetur. Adokwe ya rike Kwamishina a gwamnatin Abdullahi Adamu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel