Matar da ta auri maza uku ta zubasu a gida daya

Matar da ta auri maza uku ta zubasu a gida daya

Wata mata mai suna Ann Grace Aguti, 'yar kasar Uganda mai shekaru 36 ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta. Matar mai matsakaicin shekaru na zama ne a yankin Ngora na kasar Ugandan.

Ta yanke shawarar auren maza uku. Richard Alich, John Peter Oluka da Michael Enyeka su ne mazan da ta aura kuma ta zubasu a gida daya domin zamantakewar aure.

Jaridar kasar mai suna New Vision ta kasar Ugandan ta ruwaito labarin yadda mahaifin Aguti, Fasto Peter Ogwang ya debi dangi don korar mazajen da 'yarsa ta aura.

Aguti, mai cikin wata shida, ta bada bukkoki uku daga cikin bakwai da ta mallaka a gidanta ga mazaje ukun da take aure. An gano cewa, Aguti na da mazaje da yawa a gidanta amma ta kori sauran saboda "rashin da'a".

DUBA WANNAN: An gano abinda yasa Buhari zai wuce kasar Ingila daga Saudiyya

A martanin da Aguti ta maidawa yunkurin koran mazajen aurenta da mahaifinta yayi, ta ce, "Da farko nayi aure kamar yadda ahalina ke so. Amma kuma burina shine samun miji nagari mai sona, wanda kuma zai iya samar min da duk bukatuna a matsayin matarsa."

"Mijina ya kasance mara amfani domin ni ke samar da duk abinda ake bukata a gidan. Lokacin da na rabu dashi, sai na fara neman irin mijin da nakeso amma ban samu ba. Ko a yanzu, ni nake ciyar da mazan da na aura. Don haka ina cigaba da nema."

Wasu daga cikin mazan da Aguti ta aura sun bayyana yadda suka hadu da matarsu.. Alich, dan sanda mai murabus mai 'ya'ya 10 ya bayyana yadda ya hadu da Aguti. Ya hadu da ita ne yayin da yake dawowa daga Brac Uganda inda taje samun bashi.

"Kekenta ya samu matsala, sai na bukaci da in gyara mata. Daga gyaran ne har soyayya ta kullu inda na tsinci kaina a halin yanzu. A waccan bukkar nake rayuwa."

Oluka, daya daga cikin mazan , ya sanar da jaridar New Vision cewa, da yake kauye daya suke, ya san Aguti na da mazan aure da yawa.

"Na hadu da ita ne ina kiwon shanuna. Kamar wasa mukayi cewa zata aure ni a matsayin daya daga cikin mazanta. A hakan ne ta bani bukka daya inda nake zaune da ita," cewar shi.

"Muna rayuwa lafiya lau da kishiyoyina kusan shekara daya kenan. Banda matsala da 'kishiyoyina'. Kawai daia Aguti ce take bada kwana kuma maganarta ce umarnin garemu," Oluka ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel