Ambaliya ta shanye kauyuka 40 a jihar Adamawa

Ambaliya ta shanye kauyuka 40 a jihar Adamawa

Wasu rahotanni kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito sun bayyana cewa, ambaliyar ruwa ta shanye kimanin kauyuka arba'in na kananan hukumomi biyar da je jihar Adamawa a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sakataren hukumar bada agajin gaggawa na jihar Adamawa, Dakta Muhd Suleiman, ya ce ibtila’in ya biyo bayan mamakon ruwan sama mai yawan gaske da ya sauka a wasu sassan jihar, har na tsawon kwanaki 3.

Dakta Suleiman yace mafi akasarin kauyukan da ambaliyar ta auku a cikin su suna gaba ne da kogin Benuwe.

Muryar Duniya ta ruwaito cewa, kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa sun hadar da Girei, Numan, Fufore, Yola ta Kudu da kuma Demsa.

KARANTA KUMA: Lafiya uwar jiki: Cire kasala da sirrika 8 na ganyen gwanda ga lafiyar dan Adam

Babban jami'in hukumar bada agajin gaggawar ya kuma yi gargadin cewa, akwai yiwuwar fuskantar karin ambaliyar, a sanadiyar la’akari da yadda ruwan kogin na Benue ke ci gaba da tumbatsa, lamarin da ya haddasa yankewar hanyoyi da ke kaiwa wasu kauyukan jihar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel