Matar Tafawa Balewa da ta rage a duniya ta mutu

Matar Tafawa Balewa da ta rage a duniya ta mutu

Allah ya yi wa Hajiya Aisha, matar tsohon firaminista, Abubakar Tafawa Balewa, rasuwa a ranar Lahadi.

Hajiya Aisha ta rasu tana da shekaru 85 bayan ta sha fama da dohuwar jinya. Ta mutu ne a jihar Legas.

Ta mutu ta bar yara guda shidda da suka hada da Sadiq, Usman, Hajiya Yelwa Tafawa Balewa.

Wata majiya daga dangin marigayiyar ta shaida wa manema labarai cewa nan bada dadewa ba za a fitar da sanarwar tsare-tsaren binne ta.

DUBA WANNAN: Yakin neman zabe: "Zuma" sun tarwatsa dandazon magoya bayan PDP a Kogi, jama'a sun kaurace wa wurin taron

Kazalika, Legit.ng ta wallafa cewa tsohon shugaban jam'iyyar PDP a birnin tarayya, Abuja, Alhaji Yahaya Yunusa Suleiman, ya mutu ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba, 2019.

A cewar Aliyu Yunusa Suleiman, wani dan uwa ga mamacin, marigayin ya mutu ne da misalin karfe 4:00 na safiyar a gidansa da ke unguwar Yangoji a karkashin yankin karamar hukumar Kwali da ke Abuja.

Marigayin ya mutu yana da shekaru 54 a duniya, kuma tuni aka binne shi bisa tsarin addinin Islama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel