Bidiyo: Yadda sojoji suka sanya wani barawo ya kamo kifin oga a cikin kwata bayan ya saci takalmi

Bidiyo: Yadda sojoji suka sanya wani barawo ya kamo kifin oga a cikin kwata bayan ya saci takalmi

- Wani mutumi ya yi wanka a cikin wata kwata mai warin tsiya bayan sojoji sun tilasta shi

- Mutumin ya yi wankan ne bayan satar wani takalmi da yayi kuma Allah ya sanya ya shiga hannun sojojin

- An bayyana cewa mutumin ya saci takalmin naira dubu ashirin ne ya je ya sayar da shi naira dubu biyu

Wani bidiyo yana ta yawo a shafukan sada zumunta inda aka ga sojoji suna ta ladabtar da wani mutumi ta hanyar sanya shi yin wanka a cikin kwata saboda ya saci takalmi na kimanin naira dubu ashirin (N20,000) ya kuma sayar da shi naira dubu biyu kacal (N2,000).

Wannan mutumi da ba a bayyana sunan shi ba ya sha wahala a wajen wadannan sojojin Najeriyan bayan sun tilasta shi yayi wanka a cikin wata kwata mai datti.

A wata hira da aka jiyo a cikin bidiyon an bayyana cewa mutumin ya sayar da takalmin da ya sata na naira dubu ashirin akan kudi naira dubu biyu kacal, hakan ya sanya suka tilasta shi yayi wanka a cikin wannan kwata mai warin tsiya.

KU KARANTA: Jerin kasashe guda 10 da suka fi ko ina talauci a duniya a shekarar 2019

Wannan bidiyo dai ya jawo kace nace a shafukan sadarwa, inda mutane da yawa suke ganin bai kamata sojojin su hukunta shi ta hanyar sanya shi ya shiga kwatar ba domin cuta na iya shiga jikin shi, ko kuma ya mutu ma sanadiyyar wannan cuta da ya dauka a wajen wankan.

Wasu kuwa cewa suke yi sojojin sun yi musu daidai, domin kuwa dama ance sojoji ne maganin barayin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel