Wata jami'ar gwamnatin tarayya a arewa ta kai kudin makarantarta N200,000

Wata jami'ar gwamnatin tarayya a arewa ta kai kudin makarantarta N200,000

- Daliban jami'ar Maiduguri sun fdada tashin hankali da alhini akan tashin gwauron zabi da kudin makarantarsu yayi

- Wasu daga ciki sun fara zargin ko jami'ar ta tashi daga ta gwamnati ne ta koma ta kudi

- Kashi 70 na daliban jami'ar asalin 'yan jihar Borno ne kuma rikicin Boko Haram ya ritsa dasu

Daliban jami'ar Maiduguri na cikin jimami da alhini sakamokon tashin gwauron zabi da kudin makarantarsu yayi.

Dabo FM ta gano cewa, a ranar Talata, hukumar gudanarwar jami'ar Maiduguri ta fidda sabon jadawalin kudin makarantar daliban makarantar.

KU KARANTA: Tsoffin tsagerun Niger Delta sun yi barazanar komawa ruwa, sun bada sharadi

A zangon da ya shude, sabbin dalibai na biyan daga N30,000 zuwa N40,000 ne. Amma sabon jadawalin yanzu haka na nuna zasu biya daga kan N100,000 zuwa N200,000.

Dabo Fm ta tabbatar da cewa, daliban da zasu karanci fannin likitanci na jami'ar zasu biya N165,000 ne a sabon zangon.

Tsoffin dalibai kuwa a wancan zangon zasu sun biya N18,000 ne.

A halin yanzu dai daliban sun fara nuna damuwarsu akan wannan karin kudin makarantar. Wasu daga cikin daliban sun fara tunanin ko jami'ar ta koma ta kudi ne ba ta gwamnati ba.

Kashi 70 na daliban jami'ar 'yan asalin jihar Barno ne. Iyayensu na daga cikin wadanda suka rasa muhallinsu a halin yanzu suna sansanin gudun hijira. To da me zasu ji? Karin kudin makarantar ko kuwa rasa matsuguni da suka yi sakamakon rikicin Boko Haram da ya ritsa dasu?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel