Yanzu - Yanzu: Buhari ya sauka Najeriya daga kasar Rasha
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya daga kasar Rasha inda ya halarci gagarumin taron
- Jirgi dauke da shugaban kasar tare da mukarrabansa ya sauka ne da misalin karfe 5:25 na yammacin yau
- Bayan taron, shugaban kasar ya samu tattaunawa da shugaban kasar Rasha inda suka yi yarjejeniya maus yawa da zasu kawo habakar tattalin arziki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan gagarumin taron da yaje na Afirka a kasar Rasha. Taron ya samu halartar akalla shuwagabannin kasashe 40 tare da gwamnatoci.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ya ruwaito cewa, jirgin da ke dauke da shugaban kasar tare da sauran jami’an gwamnatin da suka masa rakiya, ya sauka ne a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 5:25 na yammacin yau.
KU KARANTA: Yanzu - Yanzu: An kara bankado wani gidan kangararru a jihar Kwara
Yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kasar Rasha, ya samu ganawa da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a ranar 23 ga watan Oktoba. Shugabannin biyu sun tattuna yadda za a karfafa alaka tsakanin Najeriya da kasar Rashan tare da maida hankali wajen kammala duk aiyukan da basu kammala ba.
Shuwagabannin kasashen biyu, sun kara da yarjejeniyar fara wasu aiyukan more rayuwa tare da fadada kasuwanci, hannayen jari, tsaro da hadin kan sojin kasashen biyu.
Kamar yadda suka tattauna, Najeriya da kasar Rasha zasu yi aiki tukuru don ganin an inganta bangaren man fetur, “domin shine jigo a tattalin arzikin najeriya.”
“Hadin kan zai ga yadda za a farfado da nakasassun matattun man fetur ta hanyar hadaka da kamfanin Lukoil na kasar Rasha,” cewar Garba Shehu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng