An goga gemu da gamu tsakanin Malami, Sanata Ahmad Lawan da Gbajabiamila

An goga gemu da gamu tsakanin Malami, Sanata Ahmad Lawan da Gbajabiamila

Babban lauyan Najeriya, kuma ministan shari’a, Abubakar Malami yayi wata ganawar sirri da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan da kuma kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila tare da wasu shuwagabannin majalisun biyu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito an gudanar da wannan zama ne don kyautata alakar bangaren dokoki da kuma bangaren zartarwa ta yadda majalisa zata kammala aiki a kan wasu kudurori, yayin da bangaren zartarwa za ta rattafa hannun a kansu domin su zama dokoki.

KU KARANTA: Yadda wani ma’aikaci ya kona ofishinsa bayan ya yi awon gaba da N1.4m

Malami ya bayyana ma taron cewa babban burinsa shine samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin bangarorin biyu don gudun kauce ma zaman doya da manja da aka samu da tsohuwar majalisa ta 8, wanda hakan ya janyo asarar kudurori da dama.

“Muna bata lokaci da da kudi wajen shirya kudurori, amma sai kaga a banza an yi asararsu, shi yasa nake so a yi aiki tare tsakanin bangaren zartarwa, bangaren majalisa da kuma bangaren shari’a idan haka ta kama a kan kudurori kafin a kai ga matakin jin ra’ayoyin jama’a don gudun kada a yi asararsu.” Inji shi.

Don haka Malam yace za su dinga aika ma majalisa kudurorin da suke aiki a kansu, don baiwa yan majalisa daman dubasu da idon basira, tun ma kafin bangaren zartarwa ta kammala aiki a kansu, idan babu matsala sai su cigaba da aiki a kai.

A nasa jawabin, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya yi maraba da wannan mataki na kyautata alaka tsakanin majalisa da bangaren zartarwa, inda yace dole ne a girmama juna tare da tuntubar juna a kai a kai.

Sauran yan majalisun da suka halarci zaman sun hada da jagoran majalisa Yahaya Abdullahi, Ajayi Boroffice, Aliyu Sabi, Emmanuel Bwacha, Sahabi Ya’u, Albert Bassey, da kuma James Manager.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng