Rahoton Bankin Duniya: APC ta jinjina wa shugaba Buhari

Rahoton Bankin Duniya: APC ta jinjina wa shugaba Buhari

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC ) mai mulki ta jinjina wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan matakin da kasar ta kai a rukunin kididdigan da Bankin Duniya ya fitar na kasashen da suka fi saukin hulda ta fannin kasuwanci a duniya.

Kamar yadda yake a rahoton da Bankin Duniya ya fitar kan kasashen da suka fi sauki wajen yin kasuwanci ya nuna cewa Najeriya a yanzu na kan mataki na 131 a duniya, inda ta tsallake kasashe 15 da a baya suke gabanta.

Bankin Duniyar ya ce Najeriya ta aiwatar da gyare-gyare wadanda suka hada da saukaka kulla yarjejeniya tsakaninta da kamfanoni.

"Hakan ya sa tattalin arzikin mutum miliyan 200 ya zama cikin mafiya kyau a duniya a jerin kasashen da suka samu ci gaba," cewar Bankin Duniya.

KU KARANTA KUMA: Shakka babu Adam Zango ya biya N46m domin karatun marayu – Shugaban makarantar Professor Ango Abdullahi

Har ila yau, a wani sako da ta aike wa manema labarai, APC ta yi maraba da yarjejeniyar da shugaban ya kulla da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, a ci gaba da taron da ake yi tsakanin Rasha da kasashen Afrika.

A cewar jam'iyyar hakan zai karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel