Yan majalisar dokokin Gombe sun bukaci yar Goje da aka zaba a matsayin kwamishina da ta wuce ba tare da yi mata tambaya ba

Yan majalisar dokokin Gombe sun bukaci yar Goje da aka zaba a matsayin kwamishina da ta wuce ba tare da yi mata tambaya ba

- An tantance diyar Sanata Goje, Hussaina Danjuma Goje a matsayin daya daga cikin zababbun kwamishinoni a jihar Gombe

- Yan majalisar dokokin jihar basu yi ma Hussaina kowani tambaya ba illa sun bukaci da ta yi ladabi ta tafi bayan gabatar da kanta

- A cewar yan majalisar, sun yanke yin hakan ne saboda kwarewarta da kuma gudumuwar da mahaifinta ya baiwa jihar

An tantance Hussaina Danjuma Goje, Diyar tsohon gwamnan jihar Gombe, Mohammed Danjuma Goje tare da sauran wadanda gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya gabatar a matsayin zababbun kwamishinoni.

Daily Trust ta rahoto cewa yan majalisar dokokin jihar Gombe basu yiwa Hussaina tambayoyi ba illa sun bukaci da ta yi biyayya ta tafi.

Yan majalisar sun yi hakan ga Hussaina ganin kwarewarta da kuma gudumuwar da mahaifinta ya baiwa jihar don ganin cigaban ta.

Ku tuna a baya cewa Gwamna Yahaya ya gabatar da Hussaina da sauran mutane 17 a matsayin kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwa na jihar.

Kakakin majalisar Abubakar Sadiq Kurba ne ya bayyana haka a wasikar da ya karanta a zaman majalisar a ranar 2 ga watan Oktoba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Najeriya za ta siyi helikoftan kai hari 12 daga Rasha bayan yarjejeniyar soji

Ibrahim Dasuki Jalo har ila yau ya kasance a cikin jerin sunayen da aka aika ma majalisar dokokin jihar. Jalo ya kasance surukin Sanata Goje. Yana auran babban yaya Husaina.

Yan Najeriya sun caccaki lamarin yin biyayya a tafi a lokacin da aka tantance ministoci da kwamishinonin da aka gabatar a matakan kasa da majalisun jihohi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel