Tambuwal ya karbi bindigogi 102 daga tubabbun 'yan bindiga a Sokoto

Tambuwal ya karbi bindigogi 102 daga tubabbun 'yan bindiga a Sokoto

- Hukumar 'yan sandan jihar Sokoto, ta bayyana cewa, ta karba bindigogi 102 daga tubabbun 'yan bindiga

- Hakan kuwa cigaba ne mai tarin yawa a fannin tsaro tare da kawo karshen ta'addanci

- Gwamna Tambuwal yayi kira ga gwamnonin sauran jihohin da 'yan bindigar suka addaba da su bi hanyar sulhu don magance matsalolinsu

Hukumar ‘yan sandan jihar Sokoto, ta ce, ta samu bindigogi 102 daga tubabbun ‘yan bindiga sakamakon samun sasancin da gwanatin jihar tayi da su.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Kaoje, ya bayyana hakan yayin mika makaman ga gwamnan jihar, Aminu Tambuwal a ranar Alhamis.

Kaoje y ace, makaman sun hada da bindigogi kirar AK47 guda 23, GMPG 7, Jaridun 2m4 da kuma bindigogin gargajiya 50 da sauransu.

KU KARANTA: Dalilin da yasa jaruma Hafsat Idris ta fashe da kuka yayin wani taro

Ya jinjinawa kokarin gwamnatin jihar karkashin shugabancin kwamishina aiyuka na musamman, Col. Garba Moyi mai murabus.

Zamu cigaba da karfafa aiyukanmu tare da kara mika hannu don ciagaba da samun tsaro mai dorewa a jihar nan.” In ji shi.

Ya kara da bukatar neman hadin kan al’ummar jihar don kawo karshen kalubbalen tsaro dake addabar jihar.

Tambuwal, ya yi kira ga jihohin da ‘yan bindigar suka addaba da su bi hanyar sulhu don kawo karshen aika-aikar ‘yan bindigar a jihohinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel