Mahaifina ya taba saida motarsa nan-take saboda in tafi Chelsea – Ola Aina

Mahaifina ya taba saida motarsa nan-take saboda in tafi Chelsea – Ola Aina

A gasar cin kofin Afrika da aka yi a kasar Masar ne ‘dan wasa Ola Aina ya fara bugawa kasarsa ta Najeriya kwallo. Jama’a da dama ba su da labarin irin fadi-tashin da Matashin ya sha a rayuwa.

An haifi Aina ne a Garin Southwark da ke Kudancin Landan a kasar Ingila. ‘Dan wasa Aina ya yi nasarar bugawa Chelsea kafin ya koma Hull City da Torinho. Ya bugawa Super Eagles a bana.

Bayan tauraruwar ‘dan wasan ta haska, ya fito ya bada labarin irin wahalar da Mahaifinsa, Olufemi Aina, ya sha domin ganin ya zama ‘dan kwallo. Yanzu haka ya na wasa a Birnin Torino.

Mahaifin ‘dan wasan ya fadawa Jaridar Aljazira cewa sun sa ran Ola Aina zai tafi Tottenham, amma aka rika yi masu wasa da hankali. A wannan lokaci kuma Chelsea ta dage da nemansa.

KU KARANTA: Yariman Saudiyya ya na neman sayen kungiyar Man Utd

Haka aka yi dai ‘dan wasan ya tafi kungiyar Chelsea. Sai dai abin ya zo wa Mahaifin ‘dan kwallon da wahala domin kuwa sai da ya rasa gidan da su ke zama a dalilin daukar Yaronsa zuwa fili.

Wata rana Olufemi ya na hanyar zuwa filin wasan Olu Aina, kwatsam sai motar ta lalace. A nan take tsohon ya saida motar, ya sa yaron na sa a cikin jirgin kasa domin ya tafi filin kwallon kafar.

“Ya biyo ni har filin horaswar Chelsea, ya tabbatar na shiga wajen wasa, sannan ya koma gida. Wannan duk domin ya tunzura ni in yi kokari, in kuma saka masu ta hanyar da ba su tunani."

Aina ne ya bada wannan labari da bakinsa. ‘Dan kwallon na Najeriya ya kuwa sakawa Mahaifin na sa domin kuwa sai da ya saya masa mota bayan ya zama Tauraron da labarinsa ya ratsa gari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng