Yadda igiyar injin nika ta datse min 'yan maraina, ta ji min ciwo a mazakuta - Bashiru Salisu, mai shekaru 14

Yadda igiyar injin nika ta datse min 'yan maraina, ta ji min ciwo a mazakuta - Bashiru Salisu, mai shekaru 14

Wani yaro, Bashir Salisu, mai shekaru 14, a jihar Bauchi ya bayyana yadda igiyar injinsa da yake sana'ar nika ta datse masa 'yan maraina.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Bashir dalibi ne da ya riki sana'ar nika yayin da yake zaman jiran sakamakon kammala karmar sakandire (junior WAEC) a makarantar gwamnati ta jeka ka dawo da ke unguwar Tudun Salmanu a cikin garin Bauchi.

Da yake sanar da NAN yadda abin ya faru daga kan gadon asitin koyar wa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, Bashir ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar yayin da yake kokarin tayar da injin, amma sai igiyar ta kama wandonsa ta fizgo shi jikin injin.

"Sakamakon kama min wandon da igiyar ta yi ne yasa na rasa 'yan maraina na sannan na samu munanan raunuka mazakuta ta.

"Na sha wuya sosai sakamakon raunin da na samu kafin daga bisani a kawo ni asibiti domin a yi min magani.

"Sai dai, abun takaicin shine yanzu na rasa 'yan maraina na, likitoci sun tabbatar da cewa babu abinda za a iya yi a kan rashinsu," matashin ya fada cikin hawaye.

Bashir ya ce ya fara sana'ar nika ne domin ya tara 'yan kudin da zai cigaba da karatu idan jarrabawarsu ta fito kasancewar iyayens talakawa ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel