Liyafa ta cigaba: Za’a fadada gidan sayar da abincin N30 zuwa kananan hukumomi 44 dake jihar Kano

Liyafa ta cigaba: Za’a fadada gidan sayar da abincin N30 zuwa kananan hukumomi 44 dake jihar Kano

- Bayan kai wata ziyara da wani dan kasuwa na jihar Kano mai suna Abdulsalam Salisu Bacha yayi zuwa gidan abincin N30, dan kasuwar ya yiwa masu gidan abincin gagarumar kyauta

- Ya basu kyautar naira dubu ashirin tare da yi musu alkawarin sanarwa da ministan noma wannan gidan abinci da suka bude

- Wannan abu ya sanya masu gidan abincin jin dadi suka kuma kuduri niyyar fadada gidan abincin zuwa sauran kananan hukumomi 44 na jihar Kano

Wani dan kasuwa a jihar Kano, Alhaji Abdussalam Salisu Bacha ya kai ziyara sabon gidan cin abinci N30 a unguwar Sani Mainagge dake nan Kano.

Dan kasuwar ya bada tallafin kudi har naira dubu ashirin ga mai gidan abincin bisa kokarinsa na aiwatar da abinda ministan noma yayi ikrari.

Sannan yayi alkawarin zai isar da wannan sakon ga ministan Noma na kasa Alhaji Sabo Nanono.

An rawaito cewa mai gidan abincin Alhaji Haruna Kassim da mai dakinsa Hajiya Sadiya Haruna sun nuna farin cikin su da wannan gudummuwa da aka basu, sannan tuni suka fara yunkurin fadada wannan gidan abinci zuwa kananan hukumomi 44 na jihar Kano domin samarwa matasa aikin yi.

KU KARANTA:

Idan zaku iya tunawa dai an bude wannan gidan abinci ne biyo bayan furucin da ministan Noma Alhaji Sabo Nanono yayi na cewar mutum zai iya cin abinci ya batse akan naira 30 kacal.

Gidan abincin ya fara ne da jarin N2,500 inda suka fara sayar da wasa-wasa wato hadin garin kwaki, sai dai izuwa yanzu jarinsu ya kai ha N8,000 da kuma ma’aikata har guda hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel