Adam Zango ya kashe N46.75m wajen daukan nauyin karatun dalibai 101
Adam A. Zango, Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa, watau Kannywood, ya dauki nauyin karatun yara 1010 a makarantar 'Professor Ango Abdullahi International School' da ke garin Zaria.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa babban jami'in kamfanin shirya fina-finai na Adam Zango, watau 'Price Zango Production Nigeria Limited', ya biya makarantar miliyan N46.75 a mastayin kudin daukar nauyin daliban na tsawon shekaru uku.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumuta (Instagram), Zango ya bayyana cewa, "ina jin dadin samun damar taimakon masu karamin karfi. Yana daga cikin burin rayuwata na taimaki jama'a, musamman kananan yara, ina jin dadin yin hakan, saboda yana saka ni farinciki.
"Ni da kamfanina kan taimaka wa jama'a ta hanyoyi da dama, ba zamu boye aiyukan alherin da muke yi ba, kuma zamu cigaba da tallafa wa rayuwar mata, yara marasa galihu da sauran talaka wa da ke fadin Najeriya.
Jarumi Adam Zango na daga cikin jaruman masana'antar Kannywood 7 da rahotanni suka bayyana cewa sun zama attajiran masu kudi.
Shugaban makarantar, Malam Hamza Jibril, ya tabbatar wa da Daily Trust cewa jarumin ya biya kudin daukar nauyin daliban.
"Eh, da gaske ne Adam Zango ya dauki nauyin karatun yara 101 a makarantar mu. Yawancin yaran marayu ne da kuma marasa karfi," a cewarsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng