Maza masu sanko sunfi ilimi da daukar hankalin 'yammata - Bincike

Maza masu sanko sunfi ilimi da daukar hankalin 'yammata - Bincike

- Wani bincike da aka gabatar ya bayyana cewa maza masu sanko sunfi daukar hankalin mata fiye da sauran maza masu gashi

- Haka kuma binciken ya gano cewa maza masu sanko sunfi sauran mutane ilimi da wayo

- Wani babban Farfesa ne mai suna Frank Muscarella na jami'ar Barry ya gabatar da wannan bincike

Sanko wani abu ne da maza da yawa suke ganin kamar nakasu ne a gare su, sai dai kuma wani bincike da aka gabatar ya bayyana cewa ba haka lamarin yake ba.

Farfesa Frank Muscarella na Jami'ar Barry ya gabatar da wani bincike, inda ya gano cewa maza masu sanko sunfi sauran maza iya mu'amala da mutane.

Wannan Farfesa ya bayyana cewa a yayin da sauran mutane ke ganin mutane masu gashi sunfi bawa mutane sha'awa, Farfesan ya ce haka suma maza da suke da sanko sunfi iya mu'amala da jama'a.

KU KARANTA: Bazan iya soyayya da budurwar da take daukar albashin kasa da N250,000 ba a wata - In ji wani saurayi

Haka kuma binciken ya gano cewa maza masu sanko sunfi bawa mata sha'awa ta inda zaka ga yawancin su suna da girman jiki da kuma karfi fiye da sauran maza. Saboda haka idan mijinki ya bukaci aske gashin kansa ki sani cewa yana kokarin inganta rayuwar sa ne.

Wannan labari da akwai alamun kanshin gaskiya a cikin shi, idan aka yi la'akari da jaruman fina-finan Amurka na Hollywood irin su, Dwayne Johnson 'The Rock', Bruce Willis, Jason Statham, Vin Diesel da dai sauran su, duka suna yin fim ba tare da gashi a kansu ba. Bayan haka bayan ban sha'awa da mutane masu sanko suke da shi, binciken ya bayyana cewa kuma sun fi sauran mutane ilimi da wayo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel