Za'a kashe mutane 16 saboda kisan daliba a kasar Indiya
Wata kotu a kasar Bangladeshe ya zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane 16 bayan samun su da laifin kashe wata daliba ta hanyar kone ta kurmus da wuta bayan sun zarge ta da yi wa malaminta kazafi na keta mata haddi.
Tun a watan Afrilun da ya gabata ne na shekarar da muke ciki, Nusrat Jahan Rafi mai shekaru 19, ta yi kacibus da ajali a wani karamin gari mai sunan Feni, wanda ke da tazarar mita 160,000 daga babban birnin Dhaka.
A rahoton da jaridar BBC Hausa ta ruwaito, malamin dai ya yaudari Nusrat zuwa kan wani soro a ranar 6 ga watan Afrilu 2019, inda kuma bayan kwana 11 ne da faruwar al'amarin Nusrat ta kai kararsa ofishin 'yan sanda da cewar ya tattaba mata jiki.
Rahotanni sun bayyana cewa, malamin da Nusrat ta zarga da yunkurin lalata da ita, da wasu mata biyu abokan karatunta, na ckin wadanda kotun ta yanke wa hukuncin kisa.
Babu shakka kisan matashiyar ya shafe tsawon lokuta yana tayar da hankalin al'umma tare da girgiza jama'a a Bangladesh, yayin da aka rinka tururuwa wajen gudanar da zanga-zanga ta neman a bi mata hakki.
KARANTA KUMA: EFCC ta fidda sunayen 'yan damfara 10 da ta cafke a Ilorin
Takaddamar wannan lamari a gaban kotu na cikin shari'o'i mafi daukar hankali da aka gudanar cikin gaggawa a kasar wadanda sabanin yanzu ake shafe tsawon shekaru kafin kammala sauraren bahasi kan zarge-zargen lalata da mata.
Sai dai lauyoyin wadanda aka daure sun ce za su gaggauta daukaka kara domin kalubalantar hukuncin kisa da kotun ta zartar a kansu.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng