Duba hoton hadadden gidan da Mustapha Naburaska ya gina

Duba hoton hadadden gidan da Mustapha Naburaska ya gina

- A makon da ya gabata ne jarumi Mustapha Naburaska ya kammala ginin gidansa

- Jarumin wasannin barkwancin ya tamfatsa gidansa ne a cikin birnin Kano

- Tun bayan rasuwar babban jarumin barkwanci, Rabilu Musa Ibro, akwai lokacin da tauraruwar Naburaska tafi ta kowa haskawa a bangaren barkwanci na masana'antar kannywood

A makon da ya gabata ne jarumi Mustapha Naburaska ya kammala ginin gidansa. Ya yi ginin ne acikin garin Kano kamar yadda muajllar Film ta ruwaito.

Tuni dai masoya, ‘yan uwa da abokan arziki suka dinga masa Allah sam barka tare da tayasa murnar wannan abu.

Duba hoton hadadden gidan da Mustapha Naburaska ya gina
Duba hoton hadadden gidan da Mustapha Naburaska ya gina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Masan'antar Kannywoood tayi sabbin shuwagabanni masu tace fina-finai

Asalin suna jarumin Mustapha Badamasi amma anfi saninsa da Mustapha Naburaska. Jarumin yayi fice a fannin fina-finan barkwanci kuma ya dade yana jan zarensa a masana’antar.

Bayan rasuwar babban jarumin da ya shahara a fina-finan na barkwanci, Rabilu Musa Ibro, an kai ga lokacin da tauraruwar Naburaska ce tafi ta kowa haskawa a bangaren.

Jarumin haifaffen garin Kano ne, yayi karatun firamare da sakandire duk a garin Kano inda ya garzaya kasar Zazzau don kara karatu kamar yadda ya sanar da jaridar Leadership.

Duk da kuwa jarumin yana cin tudu biyo ne ta fannin sana’a; yana fim kuma yana taba siyasa.

Jarumin fitaccen dan kungiyar Kwankwasiyya ne, wani bangaren jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Jarumin da bai cika shekaru arba’in ba a duniya ya kamala tankasheshen gidansa ne a satin da ya gabata a cikin garin na Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel