Masan'antar Kannywoood tayi sabbin shuwagabanni masu tace fina-finai

Masan'antar Kannywoood tayi sabbin shuwagabanni masu tace fina-finai

- A ranar Asabar da ta gabata ne aka rantsar da sabbin shuwagabannin hukumar tace fina-finai

- Dakta Ahmad Sarari ne ya tabbata shugaban kungiyar bayan da ya lashe zaben da aka yi Dutse, babban birnin jihar Jigawa

- Shugaban ya yi alkawarin fadada masana'antar har zuwa wasu jihohin Najeriya

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka rantsar da sabbin shuwagabannin kungiyar tace fina-finan Kannywood ta Najeriya. An rantsar da sabbin shuwagabannin MOPPAN din ne biyo bayan zaben kungiyar da aka yi a birnin jihar Jigawa, Dutse.

KU KARANTA: Duk da gwamnati bata zo kansu ba, wasu malamai sun rufe gidajensu na horarwa

Tsohon shugaban hukumar tace fina-finan ta kasa na yankin arewa maso yamma, Dakta Ahmad Sarari ne ya lashe zaben. Ya yi nasara ne kan abokin takararsa, Alhaji Abdullahi Maikano Usman, wanda shine shugaban kungiyar kuma ya nemi zarcewa.

Tuni Alhaji Abdullahi Maikano Usman ya aikawa da abokin takararsa kuma wanda ya yi nasara lashe zaben sakon taya murna.

Dakta Sarari dai ya yi alkawarin sake bunkasa kasuwar fina-finan hausa a kasar nan. Ya kara da alkawarin fadada tasirin masana’antar Kannywood din zuwa sauran jihohi. Ya kara da alkwarin ganin ya magance duk wasu matsalolin da suke damun masan’antar ta Kannywood.

Kungiyar MOPPAN dai kungiya ce da ke tace fina-finai da wakoki na mawaka da mashirya fina-finan Kannywood. Kungiyar kan ladaftar da duk wani jarumi ko jaruma da suka yi wa dokokinta karantsaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel