An karrama matar da tafi iya shayar da jaririnta nonon uwa a jahar Kaduna

An karrama matar da tafi iya shayar da jaririnta nonon uwa a jahar Kaduna

Shayar da nonon ga jarirai abu ne mai matukar muhimmanci ga lafiyar jarirai kamar yadda addinin musulunci ya yi nuni, haka suma masana ilimin kiwon lafiya suna baiwa mata kwarin gwiwar aiwatar da wannan tsari domin a samu al’umma mai koshin lafiya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito an karrama wata mata a jahar Kaduna wanda ta ciri tuta a tsakanin iyaye mata a jahar ta bangaren kwarewa wajen iya da shayar da jariransu na tsawon lokaci.

KU KARANTA: An tsinci gawar hafsan Sojan Najeriya a babban birnin tarayya Abuja

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata kungiya mai zaman kanta mai suna Alive and Thrive Nigeria/FHI360 ce ta karrama wannan mata mai suna Amina Abubakar wanda ta haifi jarirai yan uku, wanda a yanzu sun kai nauyin kilo 7 duk da cewa watanninsu 7 kacal, tsabar shan nonon uwa.

Kungiyar ta karrama Amina ne tare da mijinta, Dakta Ibrahim Baba saboda goyon bayan da yake baiwa matar tasa, da kuma jami’ar kiwon lafiya da take taimakawa wajen kulawa da jariran, Ramatu Ajiyana.

Da yake mika kyautar karramawar ga Aisha, shugaban Alive and Thrive, Victor Ogbodo ya jinjina ma Amina Abubakar da Ibrahim saboda nuna kwazo da azama da suke yi wajen tabbatar da jariransu sun sha ruwan nono babu kakkautawa, wanda hakan yasa suka kai nauyin kilo 7 cikin wata 7.

Baya ga iyayen yan ukun, kungiyar ta karrama uwargidar gwamnan jahar Kaduna, Aisha Ummi El-Rufai saboda rawar da take takawa wajen cigaban kiwon lafiya a jahar gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel