Shikenan fitsara ta kare: An daurawa mawakiya Nicki Minaj aure da masoyinta Kenneth Petty

Shikenan fitsara ta kare: An daurawa mawakiya Nicki Minaj aure da masoyinta Kenneth Petty

- Mawakiya Nicki Minaj ta tabbatar da daurin aurenta tare da masoyinta Kenneth Petty bayan sun shafe kusan shekara daya suna soyayya

- Mawakiyar ta wallafa wani bidiyo ne a shafinta na Instagram inda aka nuno yadda ake hidimar bikin auren nata

- A makon da ya gabata ne mawakiyar ta bayyana cewa ta gama shirye shirye tsaf domin a daura musu aure

Fitacciyar mawakiyar nan Nicki Minaj yanzu haka za ta iya bayyana Kenneth Petty a matsayin mijinta bayan shafe kimanin shekara daya suna soyayya.

Nicki Minaj ta bayyana labarin auren na su ne a shafinta na Instagram inda ta wallafa wani bidiyo da yake nuni da yadda ake hidimar gabatar da bikin auren.

Mawakiyar dai ta bayyana wannan sanarwa ne a ranar Litinin dinnan da ta gabata 21 ga watan Oktoba, inda ta sanya wannan bidiyo a shafinta na Instagram ta kuma tabbatar da ranar auren nata.

Alamu na nuni da cewa mawakiyar ta bawa masoyanta mamaki ne, inda taje aka daura musu auren nasu a boye ba tare da kowa ya sani ba.

KU KARANTA: Tirkashi: Wani saurayi ya sha alwashin kashe dan gidan shugaban kasar Amurka Donald Trump

Hakan ya zo bayan watanni biyu da mawakiyar ta canja sunanta daga Nicki Minaj zuwa Mrs Petty a shafinta na Twitter.

Idan ba a manta ba kuma a makon da ya gabata ne dai mawakiyar ta bayar da sanarwar cewa ta gama shiri tsaf domin aurar masoyinta Kenneth Petty, inda ta ce an riga har an basu lasisin auren su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel