Waka a bakin mai ita: Kwankwaso ya fadi su waye suka kai wa tawagarsa hari a Kano

Waka a bakin mai ita: Kwankwaso ya fadi su waye suka kai wa tawagarsa hari a Kano

Tohon Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, ya gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ita ce ta kitsa harin da aka kai wa tawagarsa da yammacin ranar Litinin a cikin garin Kano.

An kai wa Kwankwaso da tawagarsa harin ne a daidai gadar Sabon Titin Panshekara yayin da suke dawowa daga kauyen Kwankwaso da ke karkashin karamar hukumar Madobi.

A hirarsa da sashen Hausa na BBC, Kwankwaso ya bayyana cewa bai yi mamakin harin da aka kai wa tawagarsa ba, saboda dama tuntuni sun samu labarin ana shirya yin hakan kuma sun sanar da rundunar 'yan sanda duk abinda yake faru wa.

Duk da BBC ba ta samu jin ta bakin bangaren gwamnatin jihar Kano ba, rundunar 'yan sandan jihar ta shaida mata cewa bata da masaniya a kan rikicin da Kwankwasiyya ke ikirarin ya faru.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya halarci Sallar Juma'a domin bawa Musulmai hakuri a kan shirinsa na rushe musu Masallaci

A cewar wani jawabi da kungiyar Kwankwasiyya ta fitar ta bakin Sanusi Bature Dawakin Tofa, kakakin kamfen din Abba Kabir Yusuf, ta ce shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa wani tsohon hadimin gwamna ne mai suna Murtala Salisu, wanda aka fi sani da 'Gwarmai' shine ya jagoranci 'yan dabar da suka kai harin.

Wasu daga cikin fuskokin 'yan dabar da jawabin ya ce an tabbatar da sune suka kai harin, sun hada da Nazifi Nanaso, Tabo, Ahmadi Babba, Babale Kuffa K/Wambai, Jamilu Goje, Rambo ‘Yanmota Bakin Kasuwa, Dan-Nura Warure, Janwe, Cimutun Dodo, Shehullahi, Isa Dani Badawa, Salo Karota, K.B Soja, Ahmadun Boma Yakasai, Ayi Dan-Allah Sharada, Aminu Mai Talakawa, Musa Baba Dorayi, Umaru Sani Koki, Balele ‘Yanmota Kasuwar Kurmi, Babba Akufi, Babawo Koki, Muntaka Niga Darma, Ma’aru Goma Hanga, Bashir-Go, Danbaba Kofar Mata da Isa Kwanti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel