Hukumar NAFDAC ta koka da rashin ingancin Burodi a Najeriya
Hukumar NAFDAC mai kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya, ta koka matuka kan rashin tsayuwar daka ta mambobin kungiyar sayar da burodi da sauran dangin abinci na gasasshiyar fulawa wajen inganta sana'arsu.
Shugaban hukumar NAFDAC na kasa, Farfesa Moji Adeyeye, shi ne ya bayyana takaicin hakan a ranar Laraba yayin wani taron wayar da kan masu gidajen burodi da aka gudanar a babban birnin kasar na tarayya.
Mrs Clementina Anyakkora, babbar daraktar hukumar NAFDAC reshen Abuja, wadda ta wakilci Farfesa Adeyeye yayin taron ta bayyana cewa, binciken da hukumar ta ke gudanar wa lokaci bayan lokaci ya bankado yadda ake samun nakasun ingancin burodi musamman rashin tsafta wajen gashinsa.
Ta ce rashin tsafta a gidajen burodi da kuma sauran gidajen gashin fulawa ya tilastawa hukumar hada gwiwa da sauran manyan masu ruwa da tsaki ta hanyar gudanar da tarukan karawa juna sani da kuma wayar da kai tun daga tushe domin tabbatar da ingancin kayayyakin abinci na gasasshiyar fulawa.
KARANTA KUMA: Facebook zai fara tona asirin labaran karya
Ta kuma bayyana damuwa dangane da ya zuwa yanzu ake samun wasu gidajen burodi na ci gaba amfani da sunadarin potassium bromate da sauran kayayykin hada burodi masu haddasa fitina ga lafiyar bil Adama.
Ta ce dole ne hukumar NAFDAC ta kara zage dantsenta wajen kare fiye da mutane miliyan 170 masu ta'ammali da burodi a kasar nan daga kamuwa da cutar kansa ta hanyar haramta hada burodi da wasu sunadarai masu haifar da mummunar barazana ga lafiya.
Ana iya tuna cewa a watan Mayun da ya gabata ne aka yi hasashen karuwar farashin burodi a Najeriya yayin da masu gidajen burodi suka koka da tsadar kayan da ake hada burodin da su musamman fulawa, sukari madara da sauransu.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng